Kungiyar AIRLIN Ta Gana Da Hukumar NDLEA a Katsina: Hadin Gwiwa Don Yakar Matsalar Miyagun Kwayoyi
- Katsina City News
- 10 Sep, 2024
- 294
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Litinin, kungiyar "Advocacy Integrity and Rule of Law Initiative" (AIRLIN), wadda take da alhakin wayar da kan jama'a kan bin doka da ƙa’ida, ta kai ziyarar haɗin gwiwa ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, a ofishin shiyyar Katsina. Ziyarar ta kasance bisa nufin kulla alaƙa da kuma haɗin kai don ƙara wayar da kan al’umma kan illar ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
Ziyarar ta samu jagorancin shugaban kungiyar na jihar Katsina, Muhammad Auwal Abba, tare da sauran mambobin kungiyar, inda suka gabatar da jawaban su ga shugabannin hukumar. A cewar su, AIRLIN na da niyyar taimaka wa hukumar NDLEA wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ta hanyar shirye-shiryen fadakarwa da wayar da kai a fannoni daban-daban na rayuwar al'umma. Kungiyar ta bayyana cewa tana da shirin tattauna hanyoyin gudanar da ayyukan shirye-shiryen fadakarwa, da kuma samar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen dakile yawaitar ta’ammuli da miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin matasa.
Shugaban hukumar NDLEA na jihar Katsina, Hassan Sani Abubakar, ya yaba da wannan ziyara, inda ya ce haɗin gwiwa da kungiyoyi kamar AIRLIN yana da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar matsalar miyagun kwayoyi a jihar. Ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen ƙara inganta aikace-aikacen hukumar NDLEA da samar da nasarori masu ɗorewa wajen rage yawan masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
Shugaban ya kuma ƙara da cewa, hukumar NDLEA na ta ci gaba da samun nasarori a Katsina, musamman wajen cafke masu safarar kwayoyi da kuma tarwatsa ƙungiyoyin da ke da alaka da fataucin miyagun kwayoyi. A cewarsa, haɗin kai irin wannan na da mahimmanci domin ƙara wa hukumar ƙarfin gwiwa tare da haɗin kan al'umma wajen yaƙi da wannan muguwar dabi’a.
Kungiyar AIRLIN ta bayyana kudirinta na ƙara tuntuɓar masu ruwa da tsaki a jihar domin kafa manyan tsare-tsare na wayar da kai, musamman ta hanyar amfani da kafofin watsa labarai da sauran hanyoyin da suka dace don isar da sakon. Suna da kwarin gwiwa cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen rage matsalar miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin matasa, wanda ke jawo barna a al’umma.
Kungiyar Bisa Jagorancin Shugaban ta na Kasa Muhammad Ibrahim Gamawa tana da shugabanni (Coordinators) a dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina domin ayyukan da ta sa a gaba na kara wayar da kai, akan Matsalolin Tukin Ganganci, Lodin da ya Wuce Ƙima, Illar Ta'ammuli da Miyagun Kwayoyi, Yaki da Miyagun Ɗabi'u da Bin Doka da Oda.