Gwamnan jihar Zamfara ya Kaddamar da Asibitin Maru
- Katsina City News
- 09 Sep, 2024
- 194
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na aiwatar da ayyukan da suke da matuƙar muhimmanci da kuma fifiko.
Gwamnan ya ƙaddamar da babban asibitin da aka canja wa fasali, kuma aka inganta a Ƙaramar Hukumar Maru a ranar Asabar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Zamfara na gyarawa da samar da kayan aiki ga ɗaukacin manyan asibitocin da ke faɗin ƙananan hukumomi 14.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya duba kayayyakin more rayuwa da na’urorin kiwon lafiya da aka samar a babban asibitin.
A lokacin da yake gabatar da jawabi, Gwamna Lawal ya ce manufar gwamnatinsa ita ce samar da tsarin kiwon lafiya na zamani wanda zai dace da buƙatun jama’a ta hanyar tabbatar da samar da ingantattun ayyukan jinya kuma masu araha ga kowa.
“Ayyukan gyare-gyaren da aka gudanar a wannan asibitin sun haɗa da inganta kayan aiki don tabbatar da cewa al’ummar Maru da kewaye sun samu ingantaccen kiwon lafiya.
“Gyaran ya shafi zamanantar da tsarin ginin asibitin tare da kawo fasahohin kiwon lafiya na zamani. Wannan cikakken tsarin zai tabbatar da cewa Babban Asibitin Maru yana da wadataccen kayan aiki don kula da kowane irin yanayin kiwon lafiya, kama daga duban marasa lafiya har zuwa tiyata.
“Ma’aikatan wannan asibiti a yanzu sun samu wadatattun kayan aiki don kula da lafiya al'umma. Manufarmu ita ce samar da yanayin kiwon lafiya na zamani wanda zai biya buƙatun jama'armu ta hanyar tabbatar da cewa ingantattun ayyukan kiwon lafiya sun kai zuwa ga kowa kuma cikin araha.
“Baya ga gyare-gyaren, wannan aikin ya haɗa da samar da wutar lantarki mai nauyin kilowatt 39 don tabbatar da samar da ingantaccen wutar lantarki ga asibitin, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaba da gudanar da ayyukan jinya da jin daɗin marasa lafiya.
“Bugu da ƙari, an sanya fitulun titi guda 35 a wurare daban-daban na harabar asibitin da kewaye, domin inganta tsaro da ganin komai ƙarara, lamarin da zai sa wa duk wanda ke muhallin asibitin kwanciyar hankali.
“Ina fatan al’ummar Maru da ɗaukacin jihar Zamfara za su yi amfani da waɗannan kayayyakin gaba ɗaya. Ina umurtar ma’aikatar lafiya da ta aiwatar da isassun matakan kula da asibitin da ci gaba da gudanar da ayyukanta.”