Tatsuniya Ta 51; Labarin Wasu 'Yan Mata Biyu
- Katsina City News
- 07 Sep, 2024
- 287
Akwai wasu 'yan mata biyu, ya da kanwa, mahaifiyarsu daya, ubansu daya. Allah ya yi musu kyawu matuƙa, har wasu na cewa kyawunsu kamar na aljanu ne.
Wata rana, ƙaramar daga cikinsu ta fita kofar gida tana sanye da rigar aya. Sai wani mutum ya gifta ya gan ta, ya yi mata sallama. Da ta amsa, sai ya ce mata: "Kin san irin kyawun da kike da shi kuwa? Amma ina mamaki ganin ke ce kike rike aya."
Da ta ji wannan magana, mamaki ya kama ta. Ta ce masa: "Ai, da ka ga yayata, ba za ka ce da ni kyakkyawa ba. Domin ta fi ni kyau nesa ba kusa ba."
Mutumin ya yi dariya, ya ce: "Toh, kirawo yayar ki mu gani."
Ta shiga gida ta gaya wa yayarta yadda suka yi da mutumin. Amma yayarta ta ce: "Gaya masa ina aiki, ba zan sami damar fita yanzu ba."
Mutumin nan ya tafi. Bayan lokaci kaɗan, sai ya rikide ya koma wani mutum daban, ya sake dawowa, ya roki ƙaramar ta sake kirawo masa yayarta. Sai suka fito tare.
Da mutumin ya ganta, ya tabbatar cewa yayarta ta fi ta kyau. Bayan sun gaisa, sai ya ce mata: "Na tura kanwarki ta kirawo ki ne domin in sanar da ke ina son ki."
Jin haka ya sa ta sunkuyar da kai saboda kunya. Da murmushi ta ce: "Na gode."
Amma shi kuwa mutumin ya ce: "Amma fa gidana a bayan gari yake, ko za ki yarda mu je ki gani?"
Da fara'a ta amince. Amma kafin su tafi, sai kanwarta ta ce: "Ni ma zan bi ku, amma zan je na sanar da mahaifiyarmu tukuna."
Bakon da yayarta suka ce: "To, je ki sanar, za mu jiraki."
Bayan yarinyar ta sanar da mahaifiyarsu kuma ta amince, sai suka kama hanya. Da suka yi 'yar tafiya, ƙaramar ta yi tuntube. Sai mutumin ya ce: "Idan jini ya fito zan shanye." Ta ce masa: "A'a, jini bai fito ba."
Haka dai suka ci gaba da tafiya, har suka isa gidan mutumin. Da suka isa, sai suka lura cewa gidan an gina shi ne da gangar jikin mutum. Wannan ya sa su tsorata, amma dai suka danne tsoronsu. Mutumin ya bude ƙofa, suka shiga suka ɗan yi hira. Daga bisani, ya raka su gida.
Bayan ɗan lokaci, sai ya nemi auren yayar, aka ba shi ita. Ta tare a gidansa, kuma kanwarta ta bi ta domin ta taimaka mata a aikin gida.
Kullum, yayar ce take aiki, sai kanwarta ta kai wa mijinta abinci. Amma ba ya cin abincin da suka kai masa da miyarsu, sai ya zubar da miyar, yana cin abinci da jini. Ashe, tsafi yake yi, yana tsotsar jinin kanwar matarsa ba tare da an sani ba. Har wata rana yayar ta lura kanwarta ta rame, ta tambaye ta: "Me ya sa kike ramewa haka?"
Kanwarta ba ta san abin da za ta ce ba. Kullum abin haka yake tafiya. Har wata rana, wata mata ta zo ta ziyarce su, ta ga mijin yayar yana cin abinci da jini. Sai ta sanar da yayar abin da ta gani.
Yayar da kanwarta suka tambayi matar: "To, me za mu yi?"
Matar ta ce: "Mu tona rami, mu sa kanwarki a ciki."
Da mutumin ya daina ganin kanwarta na kawo masa abinci, sai ya tambayi matar: "Ina kanwarki? Ban ga ta kawo mini abinci ba."
Sai ta ce: "Ai ta tafi kallon wasa a kauyen kwadi."
Tun yana tambaya lokaci zuwa lokaci, har ya zama kullum sai ya tambaya. Kuma duk lokacin da ya tambaya, sai ta ce masa: "Ta tafi kallon wasa."
Bayan wani lokaci, sai ya ce wa matar: "Zan je kauyen kwadin nan in dawo da ita."
Matar ta ce: "To, na yarda. Ai ita ce take taimaka mini da aikace-aikacen gida."
Wata rana, da mijin ya fita, sai matar ta tura kanwarta gida don ta sanar da iyayensu halin da suke ciki. Ta ce wa kanwarta ta gaya musu cewa za su zo ganin gida tare da mijin. Ta kuma ce: "Su haka rami mai zurfi, su sa wuta a ciki ta ruru, sannan su rufe shi da ƙirare. Sai su yi shimfiɗa a kai, idan mijin ya zauna, zai fada cikin wutar."
Iyayensu sun shirya yadda aka ce. Da suka kama hanyar zuwa gidan surukai, sun nuna masa shimfidarsa. Bai jima da zama ba sai ya fara jin zafi. Sai ya ce: "Ina jin wani dumi-dumi, ko dai jikina ne?"
Matar ta ce: "Lallai kam jikinka ne."
Kafin ta gama magana, ƙiraren da aka rufe ramin da su suka zube, ya auka cikin ramin wuta, ya kone kurmus. Amma sai toka tasa ta zama bishiyar aduwa.
Labarin wannan bishiyar ya kai ga Sarkin gari. Sai Sarki ya yi yekuwa, ya hana kowa shan 'ya'yan aduwar. Amma wata rana matan Sarki suka ce, ba za su bari ba, sai sun sha 'ya'yan aduwar.
Daya daga cikin matan, tana da ciki, sai ta tsinki daya daga cikin 'ya'yan aduwar ta sha. Da ta sha, sai bishiyar ta biyo ta har kofar fadar Sarki.
Sarki ya shiga gida, ya tambayi matan abin da ya faru. Sai suka yi masa bayani. Sarki ya ce: "Zan yi maganin wannan hatsabibin mutum."
Sarki ya umarci Sarkin baka ya magance matsalar. Nan da nan ya hada wani turare. Da hayakin turaren ya bugi bishiyar, sai ta narke, kowa ya huta.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa:
1. Halin kirki shi ne abin duba a wurin zaben abokin zama, ba kyau ba.
2. Hatsari ne a auri wanda ba a san asalinsa ba.
Daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman