An Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Gobarar Gidan Gwamnatin Jihar Katsina

top-news


Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

Barista Abdullahi Garba Faskari, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, a madadin Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya kaddamar da wani kwamitin bincike kan gobarar da ta tashi a gidan gwamnatin jihar Katsina. A cikin jawabinsa, Barista Faskari ya nuna godiyarsa ga Hukumar Kula da Gobara ta Tarayya da sauran hukumomin tsaro da suka yi namijin kokari wajen dakile gobarar, wadda ta faru da safiyar ranar 2 ga Satumba, inda aka takaita barnar zuwa wani bangare na ofishin Gwamna.

A sakamakon wannan lamarin, Mai Girma Gwamnan Jihar, Malam Dikko Umar Radda, ya gaggauta kafa wannan kwamitin da nufin bincike tare da gabatar da shawarwari don hana sake afkuwar irin wannan.

Kwamitin, wanda ke kunshe da kwararrun mutane, ya riga ya fara aikinsa tun kafin wannan kaddamarwa.

Kwamitin na da mambobi masu muhimmanci da suka hada da:

1. Shugaban Ma’aikatan Jihar, Alhaji Falalu Bawale, wanda zai shugabanci kwamitin.
2. Injiniya Sani Magaji, Ph.D., Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri.
3. Kwamishinan Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Tattalin Arziki.
4. Kwamishiniyar Shari’a ta jihar Katsina, Barr. Fadila Muhammad 
5. Dr. Nasir Maaz, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida.
6. Kwamishinan Ma’aikatar a ma'aikatar yada Labarai da Al’adu, Malam Bala Salisu Zango Ph,D.
7. Dr.Yusuf, Sakatare Dindindin na Gidan Gwamnati.
8. Kwamandan Jiha na Hukumar Kula da Gobara ta Tarayya, Katsina. 
Da sauran su

An bawa Kwamitin ikon kiran duk wani mutum ko jami’in da yake da kwarewa da zai taimaka wajen gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

An bayar da wa’adin sati guda ga kwamitin don ya kammala aikinsa tare da mika rahotonsa ga gwamnatin jiha don daukar matakin da ya dace.

A karshe, Barista Faskari ya yabawa mambobin kwamitin bisa amincewar da aka nuna musu tare da fatan Allah ya ba su nasara wajen gudanar da wannan muhimmin aiki.

NNPC Advert