Katsina: Hukumar CSDA Ta Gudanar Da Shirin Bayar Da Tallafi Ga Unguwar Bayan Polo
- Sulaiman Umar
- 25 Aug, 2024
- 463
Daga Sulaiman Ciroma
Yayin cigaba da gudanar da ayuukan jin kai da kuma bada tallafi ga al’ummar jihar Katsina, hukumar CSDA ta gudanar da zaben tantance bukatu a unguwar Bayan Filin Polo da ke jihar jihar Katsina domin tantance irin tallafin da ya kamata ta gudanar a yankin.
Zaben tantance bukatu wanda ake kira a turance da “Patispatory Rural Appraisal” ya kasance zabe ne da wannan hukuma ke gudanarwa a kowani yanki da ya kamata a tallafawa domin gano aikin da za a gudanar daidai da bukatun al’ummar yankin.
A yayin gudanar da zaben, shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin daya daga cikin mambobin kungiyar ya yi tsokaci tare da Karin haske game da manufofi da tsare tsaren hukumar a inda ya fara da “Ina taya ku murna da kasancewarku daga cikin al’ummomi 65 da za su samu alfanu na wannan tallafi.”
“Saninku ne cewa wannan hukuma ta CSDA hukuma ce wacce take ma al’ummah tallafi kai tsaye su aiwatar da ayyukan da suka shafi bangaren ilimi wato gina makaranta ko gyarawa da abin da ya shafi kiwon lafiya kamar gyaran asibiti ko gina sabuwa da abin da ya shafi muhalli da yin hanyoyin ruwa da kuma samar da ruwan sha ta hanyar gina rijiya ko yin tuka-tuka ko yin rijiya mai amfani da hasken rana.”
Yayin da shugaban ke gabatar da jawabin, yayi bayanin matakan da hukumar ta bi wajen gano cancantar gudanar da tallafin a unguwar, ya kuma fayyace yadda tsarin gudanar da tallafin yak e, a inda yake cewa “akwai abu mai muhimmanci na wannan tallafi da ake badawa, wannan tallafi kusan abin da wannan hukuma ke badawa a aiwatar da wadannan aikace-aikace bai wuce miliyan sha biyu ba, to amma cikin miliyan sha biyunnan, al’ummah ke da alhakin bada kasha uku bisa dari na wannan kudi, kusan zai kama dubu dari uku da sittin kenan”
Sannan gabannin gudanar da zaben, shugaban ya fayyace yadda tsarin jefa kuri’un ke kasancewa yayin da za a samar da alamomi daban-daban na bukatun sannan a bawa mutanen yankin damar jefa kuri’u a wannan alamomi kana daga karshe a dauki mafi rinjaye tare da yin la’akari da adadin kudin da ke kasa wanda za ayi amfani wajen gudanar da aikin.
Ya kuma kara da cewa bayan an kamala zaben bukatun akwai zaben shuwagabannin da za su jagoranci aikin a yayin gudanar da shi inda yace ana bukatar shuwagabannin su kasance su takwas wato biyar maza da kuma uku mata.