Kungiyar Tafiyar Matasa Ta Kasa Ta Jihar Katsina Ta Fara Shirin Sauya Tsarin Siyasa – Hon. Abdulrazak Dahiru Kaita

top-news

Katsina Times 

A yau 25 ga Agusta, 2024, Hon. Abdulrazak Dahiru Kaita, shugaban riko na kungiyar Tafiyar Matasa ta Kasa, reshen Jihar Katsina, ya bayyana shirin kungiyar na sauya tsarin siyasa da manufofi ga matasa a jihar da kasa baki daya.

Hon. Kaita ya fara da mika godiyarsa ga Allah SWT bisa damar da aka ba su na jagorancin matasa, tare da jinjina ga iyayensu da sauran shugabannin kungiyar da suka ba da goyon baya wajen cimma nasarori. Ya kuma jaddada cewa kungiyar na tsaye wajen ganin an kawo gyara a harkokin siyasa da mulki.

Ya ce, “Kungiyar Tafiyar Matasa an kafa ta ne domin ceto matasa daga mawuyacin halin da aka samu matasa a cikinsa, musamman yadda aka maida su bawayi ga 'yan siyasa. Wannan tafiya ta matasa za ta ba wa matasa damar shiga harkokin siyasa da kuma karbar jagorancin al'umma."

Hon. Kaita ya bayyana cewa kungiyar na kokarin tabbatar da wakilai a kowanne mataki, har ma a runfuna (polling units), tare da shirin kafa jam'iyyar matasa (Youths Party of Nigeria) da za ta bai wa talakawa da matasa damar shiga harkokin zabe.

Ya kuma kara da cewa kungiyar na da tsare-tsare na musamman da suka hada da rage tsadar mulki, bunkasa harkar ilimi da lafiya, samar da ingantaccen tsaro, da inganta tattalin arziki ta hanyar amfani da fasaha irin su Artificial Intelligence (AI).

Daga karshe, Hon. Kaita ya yi kira ga matasan Jihar Katsina da su hada kai, su cire son zuciya, su jajirce tare da aiki da addu’a, domin samun nasarar wannan tafiya. Ya kuma yi fatan alheri ga kasar nan, yana mai cewa "ba za mu daina ba har sai mun cimma nasara da ikon Allah."

NNPC Advert