Rundunar 'Yan Sanda ta Katsina Ta Yi Wa Jami'ai 109 Ƙarin girma
- Katsina City News
- 20 Aug, 2024
- 454
Karkashin jagorancin Kwamishinan 'Yan Sanda (CP) Aliyu Abubakar Musa, Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Katsina ta karrama jami'ai 109 da aka sabunta musu mukamai. Bikin na ba da mukaman ya gudana ne a dakin taro na 'Yan Sanda da ke kan titin Kangiwa, GRA, Katsina.
Jami'an da aka daga daga mukamin Insfekta zuwa Mataimakin Sufeto na 'Yan Sanda II (ASP II) sun samu sabbin mukamansu a gaban abokan aiki, 'yan uwa, da abokai. Wannan taro ya kasance abin alfahari da girmamawa ga jajircewarsu wajen gudanar da aiki.
Yayin da yake jawabi a wajen taron, CP Musa ya gode wa Sufeto Janar na 'Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, bisa amincewa da jajircewar jami'an. Ya taya su murnar sabbin mukaman da suka samu, tare da karfafa su da su ci gaba da nuna kwarewa da sadaukarwa wajen gudanar da aikinsu.
Wannan bikin na daga cikin kokarin da Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Katsina ke yi domin karfafa jami'anta da kuma yabawa da jajircewa a cikin aiki.