Ministan Yaɗa Labarai ya rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki tuƙuru tare da shugabannin hukumomi
- Katsina City News
- 14 Aug, 2024
- 441
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar yin aiki tuƙuru tare da shugabannin hukumomi da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa.
Ministan ya umarce su da su yi aiki wurjanjan domin yaɗa bayanai kan nasarorin Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Idris ya bayyana haka ne a Abuja ranar Talata yayin da yake buɗe taron kwana ɗaya na Daraktocin Ma’aikatar da shugabannin hukumomin ta da cibiyoyin ta.
Ya ce, “Tun zuwan gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, akwai tsarin da aka yi don cimma Shirin Sabunta Fata tare da dukkanin ma'aikatu da hukumomi, tare da kuma na'urar bin diddigi don tabbatar da ɗa'a. Sashen Bayarwa da Gudanar da Sakamako (CRDCU) a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ne ke sarrafa na'urar bin diddigin.
"Dukkan ku a nan kuna da alhakin kai sakamakon mu ga wannan ofishi a matsayin shugabanni ko Jami'an Bayarwa. An shirya wannan taro ne don tabbatar da cewa mun fahimci wannan alhakin.
“Za ku iya tuna cewa ni da Babbar Sakatariya mun rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki tuƙuru tare da Shugaban Ƙasa don tabbatar da cewa za mu aiwatar da aikin ma’aikatar. An gaya mani cewa Babbar Sakatariya ta sa daraktoci su ma su jajirce wajen aiwatar da aikin.
"A yayin wannan taron, na yi ƙudiri aniyar samun shugabannin hukumomi su sanya hannu kan yarjejeniyar aiki tuƙuru su ma.”
Ministan ya bayyana cewa akwai buƙatar shugabannin hukumomin yaɗa labarai da sassan ma’aikatar su fahimci ƙoƙarin gwamnati na shirin Sabunta Fata. Wannan ya haɗa da haɓaka mafi ƙarancin albashi, lamunin ɗalibai, rance na mabuƙaci, lamunin kasuwanci, da tallafi daban-daban, ta yadda za su iya isar da bayanai kan waɗannan ga jama'a yadda ya kamata.
“Har ila yau, gwamnati ba ta bar ayyukan ta na samar da ababen more rayuwa da ayyukan jama'a a faɗin ƙasar nan ba; dole ne mu fahimci wannan yunƙurin kafin mu iya yaɗa su cikin nasara,” inji shi.
Idris ya ce ayyukan ma’aikatar har ila yau sun haɗa da ayyukan da suka shafi tsari da haɗa kai da sauran hukumomin gwamnati don yaɗa bayanan ayyukan su.
Ya buƙaci mahalarta taron da su tattauna game da wuraren da ba su da tabbas don tabbatar da cewa ba wai kawai sun aiwatar da aikin su tuƙuru ba, a'a har ma a riƙa ganin sun yi hakan yadda ya kamata.
Idris ya kuma miƙa godiyar sa ga Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Tsare-tsare, Hadiza Bala Usman, bisa yadda ta nuna sha’awar ta kan wannan aiki, ya kuma yaba da irin kyakkyawan aikin da tawagar ta ke yi a CRDCU.
Mahalarta taron sun haɗa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Ngozi Onwudiwe; Darakta Janar na hukumar talabijin ta NTA, Comrade Abdulhameed Dembos; Darakta Janar na Hukumar Kula da Gidajen Talabijin da Rediyo ta Ƙasa (NBC), Mista Charles Ebuebu; Darakta Janar na Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; Darakta Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Manajan Darakta na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Alhaji Ali Mohammed Ali, Sakatariyar Zartaswa ta Majalisar Jarida ta Nijeriya, Dakta Dili Ezughah; da daraktoci a ma’aikatar, da sauran su.