Gwajo-gwajo Ya Taya Ferfasa Badamasi Da Imam Murnar samun Sabbin Maƙamai
- Katsina City News
- 12 Aug, 2024
- 287
Mai Baiwa gwamna jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa shawara akan harkokin siyasa Hon Ya'u Gwajo-gwajo ya taya murna ga Farfesa Badamasi Charanchi da Abdullahi Imam akan muƙamin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba su wasu wurare masu mahimmanci a gwamantin tarayya..
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai baiwa Gwamna Shawara akan harkokin siyasa Hon Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya fitar Kuma aka rabawa manema labarai a Katsina.
Gwajo-gwajo ya bayyana wanda aka baiwa muƙamin wato Ferfasa Badamasi Lawal Charanchi a matsayin shugaban hukuma mai kuka da tallafawa ƙananan sana'o'i ta Nijeriya da cewa anyi abinda ya da ce a lokacin da ya da ce
Haka kuma ya bayyana cewa Abdullahi Imam ya cancanci wannan muƙami da aka ba shi a matsayin manaja mai kula da shirin tallafawa masu ƙaramin karfi a gwamantin tarayya saboda kwarewar sa na tsohon akawunta
A cewar sanarwar, muƙaman guda biyu da aka baiwa 'yan Katsina an ɗora ƙwarya a gurbin ta, musamman Ferfasa Badamasi Lawal da yake da kwarewa a fannin malanta wanda ya yi a jihar Katsina da ayyuka da ya yi wurare daban-daban kafin ya zama. Shugaban hukumar da ke kula da tallafawa masu ƙananan sana'o'i ta Nijeriya
Sanarwar ta cigaba da cewa Dakta Badamasi Lawal ya riƙe muƙamin mai baiwa gwamna shawara akan harkokin ilmi mai zurfi sannan ya yi kwamishinan ilimi na jihar Katsina da kuma kwamishina a ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautu kuma ya nuna majinta a wuraren da ya yi aiki.
"Haka kuma Alhaji Abdullahi Imam ya riƙe muƙamai daban-daban kamar a ɓangaren Banki kafin ya yi aiki a majalisar tarayya sannan ya kasance mai baiwa gwamna shawara inda kuma ya zama. Kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare na jihar Katsina" inji sanarwar
Da yake tuna irin gudunmawar da mutanen biyu suka bada a matsayin su na 'yan jihar Katsina wajen samun nasarar zaɓen 2023 a matakin tarayya da jiha, Hon. Gwajo-gwajo ya yi kira gare su da su taimakawa kokarin gwamanti wajen samar da roman dimokuraɗiyya ga 'yan Nijeriya