Matasa Na Samun Damar Inganta Rayuwa Ta Hanyar Fasahar Zamani a Katsina -Jobe
- Katsina City News
- 12 Aug, 2024
- 252
Katsina, 11 ga Agusta, 2024: Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da amfani da fasahar zamani don bunkasa rayuwar matasa a jihar. Yayin da duniya ke bikin Ranar Matasa ta Duniya ta bana, Malam Jobe ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana aiki tukuru wajen samar da damammakin fasahar Zamani, da zasu ba matasa damar inganta rayuwarsu.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kan taken Ranar Matasa ta bana, "Daga Danna Maballin Zuwa Ci Gaba: Hanyoyin fasahar Zamani na Matasa don Ci Gaba Mai Dorewa," inda ya jaddada cewa gwamnatin Katsina tana mayar da hankali wajen kawar da gibin dijital da kuma horar da matasa don su samu kwarewar da za ta basu damar yin fice a duniya ta zamani.
Malam Jobe ya yi tsokaci kan cigaban da aka samu a bangaren fasahar sadarwa a jihar, ciki har da kafuwar Hukumar KATDICT, wadda ake ganin tana taka muhimmiyar rawa wajen inganta kirkire-kirkiren matasa. Ya ce, "KATDICT yana wakiltar kudirin gwamnati na gina fasahar zamani a tsakanin matasan Katsina."
Hakazalika, Malam Jobe ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana daidaita shirye-shiryen fasaha da muradun ci gaba mai dorewa na duniya, inda ya ce ana kara samar da damammaki ga matasa domin su taimaka wajen cimma wadannan muradu.
Ya kuma kara da cewa jihar tana ci gaba da zuba jari a bangaren kayan aikin fasahar Zamani, musamman ma a fannin AI da koyon na’ura, domin baiwa matasa damar samun kwarewar da ake bukata a duniya.
A karshe, Malam Jobe ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen gwamnati domin bunkasa rayuwar matasa a jihar Katsina.