"Idan Har Nasan Dikko Umar Radda Ba Zai Yi Abinda Ya Dace ba, a Gwamnatinsa Wallahi Ba Zan Amshi Muƙamin da ya Bani ba" -Dakta Aliyu Kurfi.
- Katsina City News
- 17 Aug, 2023
- 676
Zaharaddeen Ishaq Abubakar Katsina Times
Shugaban hukumar Adana kayan Tarihi da Al'adu na Jihar Katsina Dakta Aliyu Rabi'u Kurfi ba yana haka a lokacin da ya karbi Baƙuncin Kungiyoyin Masu Sana'un gargajiya a jihar Katsina a babban Ofishin Hukumar dake Open Airthereter akan hanyar Jibiya ranar Alhamis.
A kokarinta na samar da tsaro da Doka da kuma inganta Sana'o,in Hausawa da wasanni, Hukumar a karkashin jagorancin Shugabanta Dakta Aliyu Kurfi, ya bayyanawa Mahalarta masu sana'ar ta gargajiya da suka hada da Masunta, Wanzamai, Makera, Makada, Maruna, Dukawa da Sauran su, cewa. "Yau shekaru Talatin akalla da biyu da kafa wannan Ofishin don haka Ko mutum ko Dabba ce tana bukatar a waiwayeta domin duba yanayin da take ciki." Yace bayanai sun nuna cewa tun a wancan lokacin ba'a faye taro irin wannan ba, to yanda muka zo wajen nan kuma gwamna ya yaba da tsarin da muka zo da shi da kuma tabbatarwa hukumar Tarihi da Al'adu cewa zashi bata cikakken goyon baya, don haka na tabbatar da gaske gwamna yake." Yace wallahi da ba dagaske Gwamna Radda yake ba da ni ba zan amshi wannan Muƙamin ba."
Dakta Kurfi yace Don haka ya zama wajibi muyiwa Wadannan Kungiyoyi naku tsari da Doka sana mu tabbatar kun inganta Sana'o,in ku. Dakta yace babu kamar masu sana'ar Magungunan Gargajiya da take buƙata sanya ido lura da kuma bin ka'ida da Ilimin abin sana kuma a tsaftaceta.
Dakta Kurfi ya yaba ma kungiyoyin da suka zo da kuma tabbatar masu da cewa Gwamnati zatayi tafiya dasu daidai da tsari kuma bisa Doka, sana kuma za'a kawo tsare-tsare da kowa zaiji ya gani kuma yabi domin a gudu tare a tsira tare.
Tun da farko an gabatar da jawabin Maraba daga mataimakin Sakataren Hukumar Malam Aliyu Kofar Soro.
Taron wanda yasamu halartar Shugaban Makera, Shugabannin Masu sana'ar Magungunan Gargajiya da na Islamic Herbal Medicine, Shugaban Masu Rini, da Dukawa, Masu Shirya Katan Dawaki na gargajiya, da Masu Ƙera Tandu na gargaji Wanzamai, da Sauransu.
A ranar Talata data gaba Shugaban Hukumar ya zauna da Kungiyoyin Dambe domin Tattaunawa duk a cikin shirye-shiryen Kawowa masu sana'ar tsari da gyara domin ingantawa da cigaba.