Yanda Zanga-zanga a Katsina ta rikide zuwa rikici a gidan gwamnati
- Katsina City News
- 01 Aug, 2024
- 417
Daga Muhammad Ali Hafizy, @Katsina Times
A safiyar Alhamis, 1 ga Agusta 2024, matasa daga sassa daban-daban na garin Katsina suka gudanar da zanga-zangar lumana mai taken #EndBadGovernmentInNigeria.
An fara zanga-zangar ne da misalin ƙarfe tara na safe a fadar Sarkin Katsina, mai martaba Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman. Daga nan, masu zanga-zangar suka doshi GRA zuwa fadar gwamnatin jihar Katsina.
A lokacin da suka isa bakin shataletalen gidan gwamnati, sun tsaya anan inda 'yan jarida suka yi hira da su game da dalilin fitowarsu.
Daga nan wasu bata-gari suka fara kokarin sauya yanayin zanga-zangar ta lumana zuwa tashin hankali. Aka yi bata kashi tsakanin jami'an tsaro da kuma bata-garin yayin da suke yunƙurin shiga gidan gwamnatin jihar.
Jami'an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa, harbe-harbe a sama, da watsa ruwan zafi domin dakile yunkurin bata-garin.