Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina Ta Shirya Domin Zanga-Zangar 1 ga Agusta, Ta Tabbatar Da Tsaron Lafiya Da Doka
- Katsina City News
- 29 Jul, 2024
- 381
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Katsina, 29 ga Yuli, 2024 - Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta sanar da shirinta na tabbatar da tsaron lafiya da doka yayin zanga-zangar kasa baki daya da aka shirya yi a ranar 1 ga Agusta, 2024. Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, a madadin Kwamishinan ‘Yan Sandan, CP Aliyu Abubakar Musa.
Yayin da yake amincewa da hakkin ‘yan kasa na gudanar da taron lumana, CP Aliyu ya jaddada muhimmancin tabbatar da tsaron jama'a da kaucewa take hakkin wasu. Don haka, an gudanar da taron tsare-tsare tare da shugabannin hukumomin tsaro a jihar don kara inganta matakan tsaro da ake da su.
Rundunar ta yaba wa ‘yan kasa da suka zabi janye daga zanga-zangar don hana yuwuwar tashin hankali kuma ta gode wa wadanda ke kira ga zaman lafiya don guje wa rikici.
‘Yan Sandan Jihar Katsina, tare da hadin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro, sun shirya tsaf don tabbatar da cewa ba za a samu keta doka da oda ba kafin, yayin, da kuma bayan zanga-zangar. CP Aliyu ya yi kira ga ‘yan kasa masu bin doka da su hada kai da hukumomin tsaro kuma su kasance masu kishin kasa.
Yayin da yake girmama hakkin gudanar da zanga-zanga, Rundunar ‘Yan Sandan ta yi kira ga masu shirya zanga-zangar da su tabbatar da cewa abubuwan da suka shirya sun kasance cikin lumana da bin doka. Duk wani abu da zai kawo barazana ga tsaron jama’a ko ya haifar da rikici zai fuskanci matakin doka.
Don gudanar da zanga-zangar yadda ya kamata, Rundunar ta kara yawan sintiri, ta tura sassan da suka kware a sarrafa taron jama’a, kuma ta kafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro. Ana bukatar masu shirya zanga-zangar su samar da cikakkun bayanai, ciki har da hanyoyin da aka tsara, tsawon lokacin zanga-zangar, da bayanan tuntuɓa na shugabanni don taimakawa wajen tsara tsaro da tabbatar da lafiya.
ASP Abubakar ya jaddada kudurin Rundunar na yin aiki tare da masu shirya zanga-zangar don tabbatar da taro cikin lumana da tsari.