Zamfara Ta Zamo Jihar Da Ta Fi Kowacce A Arewacin Nijeriya A Jarabawar NECO
- Katsina City News
- 25 Jul, 2024
- 485
Jihar Zamfara ta zama ta daya a Arewacin Nijeriya kuma ta biyu a faɗin ƙasar wajen samun sakamako mafi kyau a jarrabawar NECO da ake shirya wa ɗalibai masu baiwa.
Hukumar shirya jarabawar ta ƙasa (NECO) ta fitar da sakamakon Ɗalibai Masu Hazaƙa na 2024 don shiga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Suleja. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa jihar Zamfara ce ta samu mafi yawan gurbi a Arewacin Nijeriya.
A cewar sanarwar, Zamfara ta zama ta biyu a faɗin ƙasa tare da dalibai 30, yayin da jihar Anambra ta samu matsayi na ɗaya da ɗalibai 35. “Ɗaliban Jihar Zamfara sun samu mafi girman maki a jarabawar NECO na ɗalibai masu hazaƙa a cikin jihohin Arewa 19, wanda hakan ya haifar da wani gagarumin ci gaba a ɓangaren ilimin jihar,” in ji sanarwar.
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana wannan nasara a matsayin wani muhimmin ci gaba da ke nuna sauyin matsayin ilimin jihar. A karon farko, jihar Zamfara ta yi fice a matakin ƙasa, wanda ke nuna gagarumin sauyi daga matsayin da ta saba samu.
Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Suleja makaranta ce da ake horar da yara masu hazaƙa a Nijeriya, tana ƙara buɗe damarmaki ga ɗalibai masu baiwa don haɓaka iyawarsu cikin sha'awar gina ƙasa da ci gaban fasaha.
A shekarar 2024, Zamfara ta samu gurbi uku bisa ƙa’ida ta jiha kuma ta samu ƙarin gurbi 27 bisa la’akari da cancantar matsayinta a cikin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya. Wannan babban ci gaba ne, musamman idan aka yi la’akari da cewa an kafa dokar ta-ɓaci a fannin ilimi a jihar a bara.
Daga cikin yara 30 masu hazaƙa daga Zamfara, 21 mata ne, 9 kuma maza ne, wanda hakan ke nuni da yadda ake ƙara ƙarfafa ilimin 'ya’ya mata a jihar. Gwamnatin Jihar Zamfara za ta ci gaba da yin ƙoƙari wajen ganin an aiwatar da cikakken manufofin ilimi, wanda hakan zai sa a samu ƙarin nasarori ga jihar.