Gwamnan Zamfara Ya Yaba Wa Tinubu Kan Amincewa Da Ƙudirin Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Yamma
- Katsina City News
- 25 Jul, 2024
- 384
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa rattaba hannu a kan ƙudirin Dokar Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma.
A ranar Talata ne shugaban ya rattaba hannu kan ƙudirin kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC) da Hukumar Raya Kudu maso Gabas.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Gusau, mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa kafa hukumar zai ƙara samar da damarmaki na ci gaba a yankin Arewa maso Yamma.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal yana fatan hukumar za ta fara aiki cikin gaggawa domin magance tsawon shekaru na rashin ci gaban da yankin ya fuskanta.
“Ina miƙa godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa rattaba hannu a kan ƙudirin Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma ya zama doka.
“Hakan ya nuna damuwar da shugaban ƙasar ke da shi ga al’ummar yankin Arewa maso Yamma da ke cikin ƙunshi, waɗanda su ke fana da matsalar ’yan bindiga na tsawon shekaru.
“An kafa hukumar raya yankin Arewa maso Yamma ne domin ta taimaka wajen sake gina tituna, gidaje, da wuraren sana’o’in da aka lalata a lokacin rikicin da ya addabi yankin. Har ila yau, manufarsa ta haɗa da magance talauci, ƙarancin ilimi, matsalolin muhalli, da sauran abubuwan da ke hana ci gaban jihohin Arewa maso Yamma.
“Gwamnonin Arewa Maso Yamma sun haɗa kai yadda ya kamata. Kafa Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma mataki ne mai kyau, kuma za mu haɗa kai don ganin an samu nasara.”