Zanga Zangar Lumana a Karamar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina
- Katsina City News
- 20 Jul, 2024
- 536
Yanzu-yanzu masu zanga-zangar lumana a Marabar Ƙanƙara, da ke ƙaramar hukumar Malumfashi, jihar Katsina, sun datse hanya ba shiga ba fita, domin nuna ɓacin ransu kan hare-haren ta'addanci da ɓarayin daji ke kai masu a gonakinsu.
Masu zanga-zangar sun datse hanyar da ta taso daga Katsina zuwa Malumfashi da kuma wadda ta taso daga Funtua zuwa Malumfashi, lamarin da ya jefa matafiya cikin hali na rashin tabbas.
Wasu daga cikin mutanen da aka yi hira da su sun bayyana cewa ɓarayin daji sun sace tare da kashe mutane da dama a gonakinsu jiya, kuma har yanzu ba a sami gawarwakinsu ba domin yi masu sutura.