MARTANI: MUN HORAS DA MALAMAN FIRAMAREN KATSINA KWAMFUTA SOSAI KAMFANIN C&C SOFTLINK
- Katsina City News
- 18 Jul, 2024
- 400
@ Katsina Times
Shugaban kamfanin C&C Softlink, wanda ya bayar da horon ilmin kwamfuta ga malaman firamare na jihar Katsina, ya mayar da martani ga labarin da jaridar Katsina Times ta buga mai taken: "AN CIRE NAIRA DUBU UKU DON HORAS DA MALAMAN FIRAMARE KAN KAMFUTA."
Shugaban kamfanin, Mr. Chris Onyegbule, ya bayyana wa jaridar Katsina Times cewa ba kwangila aka ba shi ba, amma ya bayar da horon ne kyauta. Kudin da ya amsa daga kowanne malami na naira dubu uku da dari biyar kudin littafin koyon kwamfuta ne da kuma takardar shaida da zai ba kowa.
Mr. Chris ya ce littafin da horon zai koya shi ne yadda kwamfuta take da kuma sarrafa ta, domin kowane dan koyo ya samu ilimi mai inganci.
Mr. Chris ya kara da cewa sun kawo kwamfyutocin laptop da batura masu caji domin horon. Duk inda suka je, suna tabbatar da kowane malami ya iya bude laptop, yin rubutu, bude folder, da ajiye abin da ya rubuta, da wasu bangarori na sanin kwamfuta.
Mr. Chris ya kara da cewa sun je wuraren da hukumar ilmin firamare ta ayyana don horon, kuma sun kwashe kwanaki uku suna wannan horon.
Mr. Chris ya ce hatta kananan hukumomi masu hatsari irin su Dan Musa, duk sun je sun kuma bayar da wannan horon.
Mr. Chris ya ce duk malamin da ya halarci horon sai ya sanya hannu a takarda tare da sunansa, lambar wayarsa, da kuma sa hannunsa.
Mr. Chris ya ce irin wannan horon sun yi shi a wasu jihohi a shekarun baya, kamar su Bauchi, Jigawa, Plateau, da sauran su.