Dattawan Jihar Katsina Sun Nemi A Kirkiro ‘Jungle Battalion’ Don Magance Matsalar Ta’addanci

top-news

Kungiyar dattijan jihar Katsina ta nuna damuwarta kan halin rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, musamman a jihar Katsina, tare da yin kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kirkiro “Jungle Battalion” domin fatattakar ‘yan bindiga daga maboyarsu.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a madadin kungiyar, sakataren, Alhaji Ali Muhammad, ya zargi ministocin tsaro da shugaban kasa da rashin kai ziyara don jajanta wa mutanen jihar Katsina bisa ga kashe-kashen da aka yi kwanan nan a sassa daban-daban na jihar.

Kungiyar ta shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya samar da wasu matakai na gaggawa ta hanyar kirkiro abin da suka kira “Jungle Battalions” don kawo karshen ta’addanci a Arewa.

“Mun sha yin korafi ga gwamnatin tarayya don karfafa abin da gwamnatin jiha ke yi, amma abin takaici, gwamnatin tarayya ba ta cika alkawuranta ba,” in ji shi.

“Sun kashe daruruwan mutane a nan Katsina kuma ba wanda daga cikin ministocin shugaban kasa ya ga dacewar zuwa ya jajanta tare da iyalan wadanda abin ya shafa.”

Ya kara da cewa idan har fadar shugaban kasa tana da gaske wajen kawo karshen ta’addanci, za a iya ba da umarni ga shugabannin tsaro don fatattakar shugabannin ‘yan bindiga ko kuma su fuskanci hukunci.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan hauhawar farashin kayan masarufi, musamman abinci, inda ta ce “Farashin kayan abinci na kara hauhawa kullum, komai yana da tsada, kuma ‘yan Arewa ba za su iya samun abinci sau uku a rana ba. Wannan abu ne mai matukar muhimmanci kuma muna ba da shawara ga gwamnatin tarayya, Shugaba Tinubu yana da kunnen sauraro kuma lokacin dimokuradiyya ne, idan ministocinsa ba sa ba shi shawara mai kyau, da fatan zai cire su ya kawo mutanen da ke da kyawawan manufofi da za su taimaka masa wajen tafiyar da gwamnatinsa yadda ‘yan Najeriya za su ji dadin rayuwa.”

NNPC Advert