Wasu Kungiyoyin Addinan Sun Fi Ma’aikatun Gwamnati Rashawa – EFCC
- Katsina City News
- 15 Jul, 2024
- 462
Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede ya ce yana da shaidun da ke tabbatar da cewa wasu kungiyoyin addinan sun fi Ma’aikatun Gwamnati cin hanci da rashawa a Najeriya.
Da yake jawabi yayin da ya halarci wani taro da Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) ta shirya a Legas ranar Juma’a, Olukoyede ya buƙaci Malaman addinin Kirista a faɗin ƙasar nan da su yi amfani da Coci “ba don yin wa’azi kadai ba har ma da nuna halin kirki domin su zama abin koyi ga mabiyan su.
Shugaban na EFCC ya zargi Shugabannin addini da danne laifinsu na rashawa suna hango na wasu.
Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya ce “A makon da ya gabata ya samu hujjar ƙwato wasu maƙudan kuɗaɗe daga wata kungiyar addini.
"Sun naɗa ka matsayin Fasto, wanda a lokacin ne ya kamata ka zama babban Mutum, amma sai gashi Ba mu ma san abin da kake yi domin samun halastacciyar rayuwa ba, kawai kana zaune kana hidima da dukiyar Coci ko kuɗin Masallaci, amma baka da wata mashigar kuɗi," inji shi.
"Wasu kungiyoyin addinin sun fi Ma’aikatun Gwamnati cin hanci da rashawa, ina da hujjar hakan. Kana kallon tabo a wurin wani, bayan kaima akwai tabo a jikin ka".
Wannan na zuwa ne watanni shida bayan da Shugaban EFCC ya ce hukumar ta bankado wata kungiyar addini da ke wawushe kuɗaɗe a Najeriya.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta yini ɗaya a Abuja mai taken “Addini, Matasa, da yaƙi da cin hanci da rashawa”
Ya ce an gano cibiyar addinin ne da laifin kare wani mai safarar kuɗi bayan an gano wasu kudade da ake zargin an wawure a asusun bankin kungiyar.
"Da muka tunkari kungiyar addini game da lamarin domin gudanar da bincike sai muka samu umarni daga sama cewa mu dakatar da binciken namu,” inji shi.