FIFA Ta Dakatar da Katsina United Daga Rijistar 'Yan Wasa
- Katsina City News
- 10 Jul, 2024
- 293
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta dakatar da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Katsina United, tare da wasu kungiyoyin kwallon kafa guda ashirin da biyu daga rijistar 'yan wasa. Kungiyoyin da aka dakatar sun hada da DC Motema Pembe, TP Mazembe, Future FC, Al Masry, Zamalek SC, Horoya AC, Raja Club Athletic, Wydad Athletic Club, African Stars FC, Katsina United FC, Kiyovu Sports Association, Royal AM, da TS Galaxy FC.
Sauran kungiyoyin sun hada da Singida Big Stars FC, Tabora United, Club Africain, CS Sfaxien, Etoile du Sahel, US Monastir, Mbarara City FC, Buildcon FC, Indeni FC, da Lusaka Dynamos FC.
Bincike a shafin yanar gizo na FIFA ya nuna cewa Katsina United ta fara dakatarwar ne tun ranar 12 ga Yuni, 2024, kuma za a ci gaba da hakan har bayan lokutan rijista uku. An yi wannan hukuncin ne saboda sabawa yarjejeniyoyi da kungiyar ta yi da wasu 'yan wasa.
Hukuncin ya jefa kungiyar cikin rudani domin wasu manyan 'yan wasansu sun riga sun fara barin kungiyar domin komawa wasu kungiyoyi. Abin ya kara ta'azzara yayin da wasu 'yan wasan da aka soke yarjejeniyarsu ta baki ba su shirya komawa kungiyar ba.
Daya daga cikin 'yan wasan da ya zanta da wakilinmu cikin sirri ya ce ya samu kiran daga Manajan Kungiyar yana sanar da shi hukuncin gudanarwar na soke yarjejeniyarsa duk da yana da sauran shekara daya kafin kammala yarjejeniyarsa ta shekaru biyu.
Ya ce, "Manajan Kungiyar ya kira ni ya sanar da ni cewa ba su bukatar ayyukana kuma kada in dawo kungiyar.
"Ina da sauran shekara daya a yarjejeniyata, don haka na shiga rudani. Amma ya ce za su biya ni watanni uku domin in tafi in nemi wata kungiyar.
"To, matsayina shi ne yarjejeniyata ta riga ta kare daga hannun Katsina United, don haka za su biya ni kudina domin in tafi wani wuri in ci gaba da sana'ata," in ji shi.
Mun ciro wannan Labarin daga jaridar Daily Trust ta ranar Talata 9 ga watan Yuni, muka fassara shi zuwa harshen Hausa.