Yarjejeniyar Samoa: Tushen Rikici Kan Hakkin LGBT da Tallafin Kasashe
- Katsina City News
- 04 Jul, 2024
- 438
Katsina Times
Rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar tana kunshe da wasu dokoki da suka tilasta kasashe masu tasowa da marasa ci gaba su goyi bayan neman hakkokin Maɗigo, Luwaɗi da Auren Jinsi, (LGBT) a matsayin sharadin samun tallafi daga kasashen da suka ci gaba.
An sanya wa yarjejeniyar suna ne da tsibirin Samoa, inda aka rattaba hannu a ranar 15 ga Nuwamba, 2023. Duk da adawar kasashen da suka kiyaye darajojin Musulunci da Kiristanci, yarjejeniyar tana kara samun karbuwa.
An samu labarin tabbatar da yarjejeniyar a Najeriya ne a ranar Litinin, 1 ga Yuli, lokacin da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu ya tabbatar da sa hannu ga kudurin cigaban a wani taro da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta shirya a Abuja.
Amma a ranar Laraba, mai taimaka wa Bagudu kan harkokin yada labarai, Bolaji Adebiyi, ya bayyana cewa takardun da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannu, wadanda Ministan Kasafin Kudi ya ambata a lokacin taron EU, sun shafi cigaban tattalin arzikin Najeriya ne kawai. Ya tabbatar da cewa babu wata maganar LGBT ko auren jinsi guda a cikin takardun, yana mai cewa ba daidai bane a ce Najeriya ta amince da wadannan dabi'u.
Adebiyi ya kara da cewa abin da Bagudu ya sanya wa hannu yana da alaka da kudaden ciniki na dala biliyan $150.
Lokacin da aka tuntubi kakakin Ministan Shari’a, Kamarudeen Ogundele, game da rikicin da yarjejeniyar Samoa ta haifar, ya ce zai gudanar da bincike amma bai bada amsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa wani lauya da ke Lagos kuma Shugaban Kwamitin Hakkin Dan Adam da Tsarin Mulki na Kungiyar Lauyoyin Afrika (AfBA), Sonnie Ekwowusi, ya nuna damuwarsa game da wannan cigaba a wani rubutu da ya yi a ranar Laraba. Ya bayyana cewa yarjejeniyar Samoa tana barazana ga ikon mallakar Najeriya da Afrika baki daya.
Ekwowusi ya tambayi dalilin da yasa Najeriya ta canja ra'ayi bayan kin sanya hannu a baya. Ya kuma jaddada cewa hukumomin Najeriya suyi bayani kan dalilin da yasa suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya.
Kakakin Majalisar Wakilai, Rabiu Yusuf, ya tabbatar da cewa yarjejeniyar Samoa ba ta zo gaban Majalisar Dokoki ta kasa ba domin a duba ta.
Kungiyoyin farar hula na Afrika sun nuna damuwa game da wannan cigaba, suna mai cewa abin kunya ne ga Najeriya idan ya tabbata cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar.
Haka kuma, Abubakar Akande, Sakataren Gudanarwa na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya bayyana cewa matsayinsu game da auren jinsi guda ko LGBT bai canja ba.
Barrister Richard Kakeeto ya yi kira ga 'yan Najeriya su kalubalanci shugabanninsu game da wannan yarjejeniya, yayin da Mrs. Omoye Olaye ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye sa hannu kan yarjejeniyar.
Daily Trust ta kuma tunatar da cewa tsohon Shugaba Jonathan ne ya sanya hannu kan dokar da ta haramta dangantakar jinsi guda a shekarar 2014, wadda ta kunshi hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.