Gwamnatin Katsina ta Bayyana Matsayarta Kan Rage Kudaden Gudanarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua
- Katsina City News
- 01 Jul, 2024
- 653
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A yau Litinin, 1 ga Yuli, 2024, Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Fasaha, da Kere-kere na Jihar Katsina, Farfesa Abdul Hamid Ahmed, ya yi taron manema labarai na gaggawa.
Kwamishinan ya bayyana cewa taron manema labaran ya biyo bayan bayanin da Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ya gabatar a baya.
A cewar Kwamishinan, manufar taron ba don yin gardama da kungiyar ASUU ba ne, sai don fayyace gaskiya.
Shugaban ASUU ya koka kan rage kudaden gudanarwa na wata-wata na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua daga Naira miliyan 16 zuwa Naira miliyan 7 da gwamnatin jihar ta yi. Ya ce hakan ya sa jami’ar tana fama da matsanancin rashin kudi, kuma ba za ta iya cigaba da gudanar da ayyukanta da kudaden da ake ware mata ba.
Ya bukaci gwamnatin jihar da ta duba batun kudaden gudanarwar jami’ar don ta iya cika aikace-aikacenta na yau da kullum.
Kwamishinan ya fayyace cewa kudaden gudanarwar naira miliyan 7 da ake bai wa jami’ar a wata-wata gwamnati mai ci ta gada daga gwamnatin da ta gabata. Saboda haka, gwamnatin yanzu karkashin Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ba ta rage kudaden gudanarwa na jami’ar ko wata cibiyar ilimi ba.
Ya kara da cewa gwamnatin ta ba da goyon baya ta fuskar biyan kudaden alawus-alawus na ma’aikatan jami’ar da kuma bayar da tallafi na kudi wajen gudanar da ayyukan jami’ar. Haka kuma, gwamnatin ta saki kudade har naira miliyan 85,992,000.00 don tantance sabbin kwasa-kwasan karatu da naira miliyan 40,000,000.00 don gudanar da bikin yaye dalibai na 9 zuwa na 13.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya biya dukkan basussukan da ake bin gwamnatin da suka shafi ginin sabbin azuzuwa da dakunan kwanan dalibai a jami’ar. Bugu da kari, ya amince da kara wa’adin kwangilar saboda karin farashin kayan gini.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta kuduri aniyar cigaban ilimi a jihar, tare da tabbatar da cewa Jami’ar Umaru Musa Yar’adua za ta iya gogayya da kowace jami’a a kasar nan.
Ya kammala da kira ga jami’ar da ta ci gaba da gudanar da aikace-aikacenta yadda ya kamata, tare da neman hadin kan kowa da kowa wajen samun cigaban ilimi a jihar.