Tatsuniya ta 32: Labarin Awa Da Dawi
- Katsina City News
- 27 Jun, 2024
- 403
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Awa da Dawi suna kiwo a daji, sai wani abu ya tsoratar da su. Kowa ya kama gabansa domin neman tsira. Suka ɓace wa juna.
Da Dawi ya nemi kanwarsa bai gan ta ba, sai ya kama hanya ya tafi. Ita kuma ta nemi hanya ta rasa. Ta riga ta bata a dajin nan. Sai tafiya take ta yi, ba ta san inda za ta ba, har dare ya yi. Da ta gaji, kuma ga dare ya yi, sai ta sami gindin wata bishiya ta kwanta, har gari ya waye. Da sassafe tana kwance sai wata tsohuwa da ta yi sammakon neman ganyen miya ta tarar da ita.
Da tsohuwar nan ta ga Awa a kwance sai ta tashe ta daga barci, ta ce da ita: "Ke yarinya, me ya kawo ki nan?" Sai Awa ta kwashe labarin yadda suka yi da ɗan'uwanta ta gaya wa tsohuwa. Sai tausayinta ya kama tsohuwa, ta dubi Awa ta ce da ita: "To idan kin yarda ki zo mu tafi da ke gidana."
Nan take Awa ta yarda suka tafi gidan tsohuwa, ta ba ta masauki da abinci. Awa ta ci abinci ta koshi, ta yi wanka ta zauna. Da tsohuwa ta kalli Awa, sai ta ga yarinya ta ƙara kyau. Da ma yunwa da dauda da gajiya da tsoro ne suka boye kyaunta. Sai tsohuwa ta yanke shawarar kai wa Sarkin garin labarin Awa ko zai so ta. Nan da nan ta isa gidan Sarki, ta same shi a zaune, ta durkusa ta yi gaisuwa ta ce: "Ranka ya dade, na zo maka da wani albishir idan kana da bukata."
Sarki ya ce: "Albishi na mene ne?"
Sai tsohuwa ta ce wa Sarki: "Ina da wata kyakkyawar yarinya wadda za ta dace da kai idan za ka yarda ka aure ta."
Sarki na jin haka sai ya ce: "A kawo ta in gan ta." Da tsohuwa ta ji haka, sai ta je gida ta gaya wa Awa, kuma suka tafi fada tare. Da Sarki ya ga Awa sai ya ce zai aure ta. Ba jimawa aka daura musu aure da Sarki, ta tare a gidansa.
Awa ta haifi danta aka rada masa sunan yayanta wanda ya bata, watau Dawi. Ana nan sai Sarki ya ce kada a katse kashin dansa da ƙara domin zai ji masa ciwo, sai dai da hantar sa. Haka kuma ake yi. Kullum da safe sai a yanka shanu, a yanke hantar da huhun a ba Awa ta rika share wa yaron kashi da su.
Wata rana sai Awa ta gaya wa Sarki tana so ta ziyarci iyayenta. Sai ya tambayi sunan garinsu, ta fada. Sarki ya sa cigiyar wanda ya san garin. Aka yi sa'a, aka samu. Sai aka haɗa shi da matar Sarki da doki ya kai ta garinsu. Kafin su tafi sai aka yanka shanu aka zuba mata hanta da huhu a cikin kwarya don katse kashin dan Sarki, aka kawo kayan tsaraba masu yawa aka ba ta.
Da Awa da dan rakiyarta suka kama hanya, har Allah ya kai su garin lafiya, murna ta kama ta. Sai ta doshi gidan iyayenta, ta shiga. Mutanen gidan suka yi murnar 'yarsu ta dawo. Bayan sun huta, sai ta ba su labarin abin da ya faru har zuwa aurenta da Sarkin garin da suke. Iyayenta da sauran danginta suka yi ta murna.
Awa ta kawo kayan tsaraba ta ba iyayenta da sauran 'yan'uwanta. Suna zaune ana hira sai danta ya yi kashi, sai nan da nan ta zaro hanta za ta katse kashin yaron da ita. Da uwar ta gani sai ta ce: “Me za ki yi da wannan hanta?"
Sai Awa ta ce: “Ai da hanta ake katse kashin dan Sarki, ba a katse masa da ƙara; mahaifinsa ya hana."
Mamaki ya kama mahaifiyar Awa da ta ji wannan batu. Sai ta shiga tunanin cewa ga abin da mutum ba zai iya samu ya ci kullum ba ya zama abin katse kashin jikanta. Daga nan sai ta shiga kulla yadda za ta kwashe hantar ta cinye.
Sai uwar ta kira Awa ta ce mata: “Dauki gora ki je ki debo mana ruwa a rafi." Saboda halinta na bin iyaye, sai kawai ta ce: “To, amma kula mini da yaron nan don ba zan je rafi da shi ba." Sai kakar yaron ta ce: “To, zan lura da shi." Da ta ga lallai Awa ta tafi daukar ruwa a rafi, sai ta kwashe hantar katse wa dan Sarki kashin da ta zo da ita gaba daya, ta gasa ta cinye.
Da yaron ya yi kashi kafin Awa ta dawo daga rafi, sai uwar ta dauki ƙara ta katse masa da shi. Sai ƙaran ya yanke shi, sai ko jini ya balle yana zuba, har jinin yaron ya zube, ya mutu. Ganin jikanta ya mutu, sai ta rasa yadda za ta yi. Sai kurum ta dauki yaron ta jefa a cikin gonar kabewar da ke bayan dakinta, ta dawo cikin gida ta zauna. Jim kadan da Awa ta dawo, sai ta tambayi inda yaron yake. Ba tare da jin komai ba, sai uwarta ta ce: “Yana cikin daki yana barci."
Sai Awa ta ce: “To shi ke nan, bari in dora mana girkin abinci." Sai ta tambayi mahaifiyarta irin miyar da za ta yi musu. Sai ta ce: “Yi mana taushen kabewa." Sai ta ce da Awa ta je bayan daki ta yanko kabewa. Fadin haka ya sa Awa yin mamakin dalilin da ya sa ta fada mata haka, maimakon ta je ta yanko kabewar da kanta, to amma sai ta tashi, ta tafi bayan daki yanko kabewar. Awa na zuwa sai ta hango gawar danta a cikin ganyen kabewa.
Da Awa ta ga haka, sai ta dauki gawar danta, ta goya shi tana tafiya tana kuka. Sai ragowar jinin yaron ke gudana a cinyarsa, kuma jinin ya jika mata jiki. Tana cikin tafiya a wannan hali, sai ta hadu da yara suna kama fara sai suka ce: “Ga Awa matar Sarki." Sai suka kama waka suna bin ta, suna cewa: “Awa, Awa karbi fara, mu dauki Dawi." Sai ta amsa musu: “Dawi yana barci." Sai suka kara cewa: “Mene ne ke gudu a bayanki kamar jini?" Sai ta ce: “Ba jini ba ne, fitsarin dana ne." Sai suka ce: “To mene ne a idanunki kamar hawaye?" Sai ta ce: “Ba hawaye ba ne, yanayin idanuna ne."
Da ta wuce yaran, haka ta yi ta tafiya cikin kuka da bakin ciki har ta isa kusa da garin da uban Dawi yake sarauta. A bakin garin ne Awa ta hadu da wata mace, wadda ta tambaye ta abin da ya same ta. Sai ta ce wa matar: “Ai dana ne ya rasu kuma ban san abin da zan gaya wa Sarki ba." Sai matar ta ce wa Awa: “Ba komai, kwantar da hankalinki. Idan kin je gida kada ki gaya wa kowa abin da ya faru. Ki dauki danki ki kwantar da shi a tsakar daki. Daga nan sai ki dauki korai biyu, ki zuba dawa a ciki, ki tsaya a kan yaron, ki fara shuka dawar. Wani zakara zai shigo ya tsaya a kan yaron, sai ki kama shi ki yanka, ki dafa. In ya dafu sai ki debi romonsa ki zuba wa yaron a baki zai tashi."
Awa ta yi godiya, ta kama hanya har ta isa gida. Ta kuma yi abin da matar ta gaya mata. Sai zakaran ya zo ya hau kan yaro; sai ta yi ihu ta fara fada. Ta sa yaran gidan Sarki su kama shi don a yanka. Suka kama shi, aka yanka, ta dafa, sai ta debi romon ta diga wa yaron a baki.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa:
1. Ceto daga Ubangiji yakan zo ta kowane hali.
2. Zarmewa wajen kula da yaro takan janyo masa bala'i ta fuskar da ba a zata ba.
3. Mai rabon ganin badi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.
4. Mai arziki ko a kwara ya saida
Mun ciro wannan labarin daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman