Jawabin Gwamnan Katsina a Taron Zaman Lafiya da Tsaro na Arewa Maso Yamma
- Katsina City News
- 25 Jun, 2024
- 437
Mai girma Mataimakin Shugaban Ƙasar Tarayyar Najeriya, Masu girma Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yamma, masu girma Jakadun Ƙasashen Waje da ke wannan wuri, Jami’an Sojoji, ‘Yan Sanda, da sauran Jami’an Tsaro da aka wakilta, Masu Martaba Sarki, da sauran jama'a maza da mata, ina yi muku barka da zuwa wannan babban taron zaman lafiya da tsaro na Arewa maso Yamma.
Na tsaya a gabanku ne a yau tare da jin kwazon aiki da jajircewa yayin da muke taruwa don tunkarar wasu matsalolin da ke addabar yankinmu na Arewa maso Yamma da muke kauna. Tarihi, al'adunmu, da burinmu na hadin gwiwa sun hada mu, kuma wannan hadin kai ne ya kamata mu yi amfani da shi wajen tunkarar matsalolin rashin tsaro.
An fara taron Ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma jim kadan bayan an zabe mu a ofis. A matsayinmu na zababbun Gwamnoni, mun gana, muka amince da mu tinkari matsalolin da muke da su tare. Rashin tsaro ya kasance abin damuwa a fili ga kowa, kuma mun amince da yin aiki kafada da kafada don magance matsalolin. Mun kuma duba bunkasa noma da samar da wutar lantarki a yankin da nufin bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin jama'ar mu. Mun ziyarci shugaban bankin raya Afirka a ƙungiyance domin neman tallafi. Har ila yau, kwanan nan mun gana da shugabannin Majalisar Ɗinkin Duniya don bin tsarin ci gaba na yanki. Sannan yunkurin da muke yi na magance matsalar tsaro ya kai mu birnin Washington D.C domin halartar taron tattaunawa da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta hada, inda muka sanar da su shirin da muke yi na gudanar da wannan taro a gida.
Gwamnonin Arewa maso Yamma yanzu ‘yan uwantaka ce a gabanmu da burin samar da zaman lafiya da tsaro da wadata ga al’ummarmu. Mun wuce rarrabuwar kawuna a siyasance, mun kuma mai da hankali kan kokarin hadin gwiwa don ci gaba tare da aiwatar da ayyukan da jama’ar jihohinmu suka dora mana a daidaikun mu.
Yaki da rashin tsaro da farko nauyi ne na Tarayya, kuma ina mika godiya ga shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu bisa jagorancinsa. Na tuna zantawa ta da shi bayan wani hari da aka kai a watannin baya da kuma martanin da ya yi cikin gaggawa kan lamarin. Ya ci gaba da yin hulda da ni a kan wannan al'amari, kuma ya himmatu wajen tabbatar da kare rayuwa da harkokin neman abincin jama'ar yankin da ma kasa baki daya. Ina son mika godiyata ga shugabannin sojojin Najeriya da na sojojin sama kan yaki da rashin tsaro da suke yi a Katsina ka’in da na’in. Ina kuma mika godiyata ga shugabannin rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro da suke aiki tare domin kare lafiyar al’ummarmu. Zan yi amfani da wannan damar domin mika ta'aziyyata ga jaruman da suka rasu.
Ina kuma son in bayyanar da sanin irin kokarin da Majalisar Dokoki ta kasa ke yi na kafa Hukumar Cigaban Arewa maso Yamma, wadda ke da nufin inganta ci gaban da ya hada yankin. Wannan yunƙurin abin yabawa, zai samar da albarkatun da ake buƙata don yaƙi da rashin tsaro ta hanyar matakan da ba na motsa jiki ba.
Ba mu kadai muke yaki da rashin tsaro ba. Ina so in yi amfani da wannan dama don nuna jin dadina ga hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya wajen shirya taron da kuma mai da hankalinsu ga yankin Arewa maso Yamma. Ina kuma gode wa dukkan manyan baki na kasashen waje da suka halarci taron nan a yau. Taimakon ku kai tsaye da kuma wanda ba na kai tsaye ba, zai yi matukar amfani wajen neman zaman lafiya da ci gaba.
Fashin daji ya yi wa al’ummarmu kaca-kaca. Ya kawo cikas ga rayuwa, da dakile harkokin tattalin arziki, da sanya tsoro a tsakanin al’ummarmu. Ba za mu iya barin wannan barazanar ta zama ita ke ayyana yankinmu ba. A matsayinmu na shugabanni, dole ne mu ɗauki matakai da yawa waɗanda suka haɗa da tattara bayanan sirri mai ƙarfi, aikin ‘yan sanda, da amfani da manyan fasahohin tsaro. Bugu da kari, dole ne mu inganta karfin jami'an tsaron kasarmu ta hanyar ci gaba da inganta horonsu da ba su isassun kayan aiki.
Domin yaƙar fashin daji yadda ya kamata, muna buƙatar ƙarfafa hanyoyin sadarwar mu. Wannan yana nufin inganta tsarin sa-ido, saka hannun jari a fasahar zamani kamar jirage marasa matuka da hotuna na tauraron dan adam, da haɓaka daidaituwa tsakanin hukumomin tsaro daban-daban. Dole ne kuma mu samar da ingantattun hanyoyin sadarwa don tabbatar da mai da martani kan duk wata barazanar tsaro kan lokaci.
Duk da haka, magance ta'addanci ba alhakin hukumomin tsaron mu ne kawai ba. Dole ne mu yi hulɗa tare da al'ummomin gida, sarakunan gargajiya, da shugabannin addini don haɓaka al'adar haɗin gwiwa da amincewa. Haɗin gwiwar al'umma yana da muhimmanci wajen tattara bayanan sirri masu aiki don dakile ayyukan aikata laifuka. Yawancin jihohin yankin sun riga sun kafa rundunoni na tsaro na al'umma inda suke aiki kafada da kafada da jami'an tsaro na ƙasa don kare al'ummominsu. A Katsina, mun kaddamar da Rundunar sa ido ta al’umma (Community Watch Corps). Jihohin Zamfara da Sokoto su ma sun kaddamar da shirye-shirye masu inganci, yayin da Kaduna ta riga ta yi wani shiri. Galibin Jihohin yankin yanzu haka sun kafa cikakken Ma’aikatun tsaro na cikin gida tare da mayar da tsaro wani bangare na ayyukansu na gudanarwa a matakin jiha.
Bugu da kari, dole ne mu magance tushen matsalar fashin daji, wanda galibi yakan samo asali ne daga tabarbarewar tattalin arziki da rashin damammaki. Koyar da sana'a, samun damar aiki, da tallafi ga kanana da matsakaitan masana'antu na iya taimakawa wajen karkatar da mutane masu rauni daga ayyukan miyagun laifuka.
Yankinmu yana da damar zama kwandon abincin al'umma, duk da haka muna fuskantar manyan kalubale wajen samun wadatar abinci. Rikicin 'yan fashin daji ya yi matukar tasiri ga ayyukan noma, ya jawo rage yawan amfanin gona da karin farashin abinci. Don magance wannan, dole ne mu saka hannun jari a ayyukan noma na zamani, mu tallafa wa manoma masu ƙaramin ƙarfi, da inganta hanyoyin samar da kayan noma da samar da lamuni.
Muna bukatar mu ba da fifiko wajen bunkasa ababen more rayuwa na karkara, kamar tituna, tsarin ban ruwa, da wuraren ajiyar kayan amfanin gona. Inganta hanyoyin karkara zai saukaka jigilar kayan amfanin gona zuwa kasuwanni, da rage asarar kayan bayan girbi da kuma kara kudin shigar manoma. Haɓaka tsarin ban ruwa zai ba da damar noma a duk shekara, rage tasirin yanayin ruwan sama da kuma tabbatar da samar da abinci daidai gwargwado.
Dole ne kuma mu karfafa gwiwar matasa a harkar noma ta hanyar shirye-shiryen karfafawa da bullo da sabbin dabarun noma. Fasahar noma ta zamani, kamar ingantaccen aikin noma, na iya haɓaka yawan amfanin gonar da za a samu. Dole ne kuma mu haɓaka ɗaukar hanyoyin noma masu yafiya tare da yanayi don rage tasirin sauyin yanayi kan ayyukan noma.
Haka kuma, dole ne mu tallafa wa manomanmu ta hanyar ba su damar samun rance mai araha da tsarin saka hannun jarin noma. Wadannan matakan za su taimaka musu wajen saka hannun jari a cikin ingantaccen iri, takin zamani, da kayan aiki, da kara yawan amfanin gona da kudaden shiga. Magance matsalolin aikin gona na iya haifar da karuwar tsaro a yankin da kuma ƙasa baki ɗaya.