Gwamnan Zamfara Ya Jaddada Bukatar Hadin Gwiwa Don Magance Matsalar Tsaro a Taron Arewa Maso Yamma
- Katsina City News
- 25 Jun, 2024
- 321
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Litinin, Gwamna Dauda Lawan Dare na jihar Zamfara ya halarci taron tsaro na farko na Arewa Maso Yamma da Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Katsina. Taron ya gudana a dakin taro na banquet a jihar Katsina, inda aka tattauna batutuwan tsaro tare da sauran gwamnonin yankin.
A yayin gabatar da jawabinsa, Gwamna Dare ya bayyana yadda matsalar rashin tsaro da kuma amfani da miyagun kwayoyi suka addabi jihar Zamfara fiye da shekaru ashirin, lamarin da ya shafi rayuwar al’umma da ci gaban tattalin arziki. Ya nuna kwarin gwiwa cewa sakamakon wannan taron zai taimaka wajen tsara ingantattun manufofi da dabarun magance wadannan matsaloli.
Gwamnan ya gode wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilta, bisa jajircewarsa wajen yakar 'yan bindiga da sauran laifuka a yankin Arewa Maso Yamma da Najeriya baki daya.
Haka zalika, Gwamna Dare ya yaba da goyon bayan UNDP Nigeria, inda ya bayyana cewa kwarewarsu da sadaukarwarsu suna da matukar muhimmanci wajen nemo mafita na dindindin ga matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Bugu da kari, Gwamnan ya taya Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma, Mallam Umar Dikko Radda, murna bisa jajircewarsa wajen hada kan yankin domin yakar 'yan bindiga, tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayansa ga wannan manufa.
Taron ya samu halartar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya, 'yan majalisa daga yankin, Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa (NSA), Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), shugabannin tsaro na kasa, shugabannin gargajiya, mambobin jakadun kasashen waje, jami'an UNDP, shugabannin masana’antu, da sauran fitattun ‘yan Najeriya.
Hotuna: Gwamnatin jihar Zamfara