Sufeto-Janar Na 'Yan Sanda Ya Ziyarci Rundunar 'Yan Sanda Ta Katsina
- Katsina City News
- 24 Jun, 2024
- 441
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar 24 ga Yuni, 2024, Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya ziyarci rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina, inda ya yaba wa rundunar bisa nasarorin da ta samu wajen yaki da laifuka da inganta tsaro a jihar. Ya kuma bukaci jami'an da su ci gaba da kasancewa jakadu nagari na rundunar 'yan sanda ta Najeriya.
IGP Egbetokun ya kara karfafa guiwar jami'an da su kasance masu jajircewa, aiki tukuru, da kuma sadaukarwa ga aikinsu, yana mai tabbatar musu da cikakken goyon bayan gwamnatinsa a yakin da ake yi da dukkan nau'ikan laifuka a jihar.
Kwamishinan 'Yan Sanda na jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya tarbi IGP cikin girmamawa, inda ya gabatar masa da bayanin halin tsaro da nasarorin da rundunar ta samu. Ya kuma gode wa IGP bisa goyon baya da jagoranci da ya kasance ginshikin nasarorin rundunar.
Hotuna: 'Rundunar 'Yansandan Najeriya reshin jihar Katsina