Tatsuniya Ta 31: Labarin 'Ya'yan Sarki Da Kadangare
- Katsina City News
- 21 Jun, 2024
- 398
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani Sarki da 'ya'yansa mata su biyu kyawawa. Amma tun suna kanana ya hana su fita waje domin tsaron lafiyarsu. Kullum suna gida har suka girma, suka isa aure. Ganin sun kai munzalin aure, sai ya bari suka ɗan fara fita waje.
Ana nan, rannan dai Sarki ya ce zai aurar da su. Manema suka fito. Wannan ya zo, a ce a'a, bai yi ba. Wancan ya zo, a hana shi. Wata rana dai sai Sarki ya ce a tara mutane, duk wanda ya kira sunan ɗaya daga cikinsu, to shi za a ba wadda ya faɗi sunanta. Shi ke nan aka sa ranar tara mutane don a ji wanda zai faɗi sunan.
Matasa da sauran waɗanda ba su wuce auren budurwa ba, kowa ya shiga neman sunayen 'yan matan; abu dai ya gagara. Sai Biri ya sami labari kuma ya ce ya san dabarar da zai yi. Sai ya je ya samo mangwaro nunannu kyawawa guda biyu. Da ya make mangwaron nan biyu, sai ya garzaya cikin lambun Sarki inda yaran suke hira, ya zauna a kan bishiyar da suke zama a gindinta ya shiga jira.
Da suka fito, sai ɗaya daga cikin 'yan matan ta je gindin bishiyar da Biri yake kai, sai ya jefa mangwaro ɗaya. Da ta gani sai ta ɗauka ta ce: "Kirindi, zo ki ga wani nunannen mangwaro na samu."
Wannan ya sa Biri murna saboda ya ji sunan ɗaya daga cikinsu. Da ɗayar ta doshi wajen wadda ta kira ta don ta je ta ga mangwaron Kirindi, sai ya jefa ɗayan mangwaron, sai ita ma ta gan shi. A cikin murna da doki ta ce: "Ai ni ma na samu Karanda."
Biri na nan sai ya kama murna yana cewa: "Yawwa ai ni zan aure su tun da na ji sunayensu."
Da lokacin da Sarki ya yanka wa mutane ya cika, sai aka tara mutane ana tambayar su ko sun sami sunan 'yan matan. Wannan ya zo ya ce kaza ne, a ce masa a'a, wancan ma ya zo bai ci nasara ba. Haka dai aka yi ta fama har aka zo kan malam Biri. Ana zuwa kansa sai ya ce: "Kirindi da Karanda." Aka ji a cikin rada saboda tsoro.
Sai Kadangare da ke gefensa ya ji, sai kawai ya yi farat da ƙarfi ya ce: "Kirindi ce da Karanda."
To shi kuma Sarki ya riga ya yi alkawarin duk wanda ya faɗi sunayensu, zai ba shi su aure. Ba tare da bata lokaci ba, aka ba Kadangare auren 'ya'yan Sarki.
Ashe Biri ya ji haushin kwacen da Kadangare ya yi masa, kuma ya sami lava sai ya ɗauki fansa a kan Kadangare. Saboda haka bayan an gama bikin amaren Kadangare sun tare a gidansa, sai rannan Biri ya haura dangar gidan gonar Sarki inda Sarki ke kiwo. A cikin dabbobin da Sarki ke kiwo kuwa, akwai wata babbar kazarsa wadda ya fi so a kan duk sauran abubuwan da yake kiwo a gonar. Sai Biri ya kama wannan kaza ya yanka, ya fige, ya dafa ya cinye. Da ya cinye ya sha ruwa, sai ya kwashe duk gashinta da kasusuwanta ya je ya haura dangar gidan Kadangare ya zuba.
Gari na wayewa, sai labari ya je ga Sarki cewa an sace masa kaza. Sai ya sa fadawa su bi gida-gida su nemo kazar nan kafin azahar. Fadawa na shiga gidan Kadangare, sai suka tarar da gashin kazar Sarki da kasusuwa. Suna ganin haka, sai suka kai wa Sarki labari. Saboda kunya da ƙara irin ta manya, da Sarki ya ji cewa a gidan surukinsa ne aka sami gashi da kasusuwan kazarsa, sai ya ce a bar maganar, kuma ya hana a hori Kadangare.
Biri dai bai ji daɗin haka ba. Duk domin ya yi ramuwar gayya, sai ya yanka akuya ya dafa aka yi romo mai kayan yaji. Ya ɗauka ya kai gidan Kadangare, romo da naman akuya suna tafasa saboda zafi. Da Kadangare ya buɗa mazubin, sai ya ga naman akuya da romo, ga kamshinsa ya cika gari. Sai ƙwadayinsa ya tashi, bai yi wata-wata ba sai ya kai bakinsa. Yana ɗosana bakinsa kuwa sai ya ƙone, ya ja baya. Matansa na fitowa sai hankalinsu ya tafi kan mazubin nan. Da suka buɗa, suka ga naman akuya ne a cikin romon da ya sha kayan yaji, sai su ma suka kwasa, suna kaiwa bakunansu sai zafi ya sa kowacce ta kwala ihu, ta tofar da wanda ta guntsa.
Dukkansu uku, watau Kadangare da matansa biyu ba wanda bai ƙone ba. Da Biri ya ga haka, sai ya fita daga inda ya make, ya kama hanya ya tafi yana dariyar ƙeta da jin daɗi, ya bar su da jinya.
Kurunkus.
TUSHE: Mun ciro wannan labarin daga Littafin "TASKAR TATSUNIYOYI" Na Dakta Bukar Usman.