Hukumar Hisbah ta Katsina Ta Bayyana Sabbin Dokoki Ga Masu Gidajen Hotel a Jihar
- Katsina City News
- 20 Jun, 2024
- 493
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta bayyana sabbin dokoki ga masu gudanar da hotel a cikin jihar, a wani mataki na tabbatar da tsaro da kuma kare al’umma daga abubuwan da suka saba wa doka da al'adun jihar.
Wannan ya biyo bayan kafa da kaddamar da Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta hannun Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raddah, PhD.
Hukumar ta lura da yadda wasu daga cikin masu hotel ke gudanar da ayyukansu ba tare da bin ka’ida ba, wanda hakan ke kawo rashin da’a a cikin al’umma. Saboda haka, Hukumar ta tsara dokoki masu zuwa ga masu hotel a jihar:
1. Duk masu hotel a jihar su tabbatar da tantance sunayen bakin da suka shiga, kuma su tabbatar da cikakken bayanin kowane bako, da ya sauka a hotel dinsu.
2. Tawagar Hukumar Hisbah za ta rika duba takardun bakin lokaci-lokaci.
3. Haramun ne a sauke yara ‘yan kasa da shekara 18 a hotel.
4. Haramun ne a bayar da daki guda ga mata biyu ko ‘yan mata.
5. Masu hotel su tabbatar da cewa babu amfani da miyagun kwayoyi a cikin harabar hotel, kuma su kai rahoto ga Hukumar Hisbah ko NDLEA idan an samu hakan.
6. Masu hotel su nemi izinin Hukumar Hisbah kafin shirya kowane taro a cikin hotel.
7. Haramun ne shan giya ko sayar da ita a cikin harabar hotel.
8. Karya dokokin da aka zayyana daga 1 zuwa 7 na iya janyo rufe hotel din har abada.
A ƙarshe, Hukumar ta bukaci duk masu hotel da su bi wadannan dokoki domin tallafawa Hisbah wajen kawar da munanan dabi'u a Jihar Katsina.