Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke Ya Bada Tallafin Sallah Ga Wasu Ɓangarorin al'umma a Katsina.
- Katsina City News
- 16 Jun, 2024
- 305
Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam'iyar PDP a zaɓen 2023 Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke ya bada tallafin Sallah ga wasu kungiyoyi a Katsina
Gudunmawar ta haɗa da kuɗaɗe domin yin hidimar Sallah ga fiye da mutum 1,000 ta yadda zasu samu damar gudanar da shagulgulan babbar Sallah lafiya.
Haka kuma wannan tallafi ya isa ga marayu da jawarawa da masu buƙata ta musamman da sauran ɓangarorin al'ummomi a cikin jihar Katsina baƙi ɗaya.
Kazalika Sanata Yakubu Lado ya raba irin wannan gudunmawa ga wasu daga cikin 'ya 'yan jam'iyyar PDP ta jihar Katsina da kuma 'yan jaridu masu aikawa da labarai.
Da yake ƙarin haske game da wannan tallafi, Sanata Yakubu Lado ya ce yin hakan na da nufin ragewa jama'a raɗaɗin tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasa baƙi ɗaya.
Ya ƙara da cewa Kuɗaɗen da aka bayar wasu za su sayi kayan abinci domin su samu damar gudanar da bikin Sallah cikin yanayi mai dadi da walwala.
Haka kuma Sanata Yakubu Lado ya ce gidauniyar sa ta fara biyawa ɗalibai kuɗaɗen jarabawar NECO ta shekarar 2024 a shiyyar ɗan majalisa uku da ake da su a jihar Katsina
"Ina da tabbacin biyan kuɗaɗen zai taimakawa Iyaye su samu sauki tare da baiwa ɗalibai damar faɗaɗa karatun su idan sun kammala sikandire" inji shi
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tallafin sun bayyana cewa hakika tallafin ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar shi a cikin al'umma.
Saboda haka sai suka miƙa godiyar su ga Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke bisa wannan karanci da ya nuna masu a irin wannan lokaci mai wahala.