Gwamnan Zamfara Ya Koka Kan Rashin Taimakon Hukumar Tsaro a Yaki da 'Yan Bindiga

top-news

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya koka kan yadda 'yan sanda da sojoji suka yi sakaci wajen yaƙi da 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi kai tsaye a shirin **Sunrise Daily** na gidan talabijin na **Channels TV** a ranar Talata.

Ya ce salon hukumomin tsaron Gwamnatin Tarayya ya sa aka samar da Rundunar Tsaron Jihar masu suna ‘Askarawan Zamfara'.

Gwamna Dauda Lawal ya ce, “Mu a matsayinmu na gwamnoni, ba mu da iko a kan sojoji, ba mu da iko a kan 'yan sanda da jami’an tsaron farin kaya, shi ya sa galibi abin ke sa mu cikin damuwa.

"Za ka ga a lokacin da muke buƙatar waɗannan dakarun tsaro, ba za a same su ba, bisa haka ne muka ga mafita kawai mu kafa rundunar mu ta kanmu."

Gwamnan ya bayyana cewa za a iya magance 'yan bindiga, waɗanda suka mayar da garkuwa da mutane sana'a, cikin makonni biyu idan aka yi niyyar hakan.

"A cikin mako biyu za su zama tarihi amma ba a shirya hakan ba a siyasance, mun san su waye 'yan bindigar nan kuma mun san wurin da suke rayuwa," in ji Dauda Lawal.

Gwamna Lawal ya yi zargin cewa wasu abokan hamayyarsa na siyasa suna tattaunawa da 'yan bindiga ba tare da saninsa ba.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya san ainihin waɗanda ke tattaunawa da 'yan bindigar, sai ya ce, "Duk abin da suke yi mun sani."

NNPC Advert