Al’ummar karamar hukumar Kafur na cike da farin ciki tare da mika sakon godiya ga gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda
- Katsina City News
- 11 Jun, 2024
- 686
Tare da mai ba shugaban kasa shawara akan harkar siyasa, Hon. Ibrahim Kabir Masari, wani matashi gwagwaren danejin Katsina, Hakimin Mahuta, ya bayyana farin cikinsa.
Al’ummar karamar hukumar Kafur, maza da mata, sun nuna farin cikinsu ganin yadda aka yi nazari wajen zakulo wanda al’umma suke da bukata a wannan lokaci.
Tabbas, gwamnatin jihar Katsina ta yi abin yabo wajen zakulo waɗanda suka dace su zama shugabannin kananan hukumomi.
Da wannan, al’ummar karamar hukumar Kafur suna mika godiyarsu bisa tabbatar da Hon. Surajo Bature Dankanjiba a matsayin halattaccen dan takarar chairman na karamar hukumar Kafur.
Allah ubangiji ya sa ya zama alheri ga karamar hukumar Kafur da kasa baki ɗaya.
Gwagwaren Danejin Katsina Hakimin Mahuta