TASIRIN HADIN KAI TARE DA GUDANAR DA AYYUKAN GAYYA
- Katsina City News
- 11 Jun, 2024
- 446
Hadin kai yana da matukar amfani da tasiri a cikin al'umma. Dashine al'ummar ke tsayawa su fahimci tareda tunkarar duk wani kalu-bale dake iya kawo barazana ga cigaban tattalin arziki da walwalar al'umma.
Yashe magudanan ruwa da gyarasu na daga cikin muhimman ayyukan da al'umma zata iya gudanarwa ta hanyar AYYUKAN gayya domin magance barazanar almbaliyar ruwa da cushewar wadannan magudanan ka iya jazawa.
Wasu ayyukan na farawane daga matakin kwatoci na kofar gidaje da kananan kwalbatoci, yayinda wasu sai anhadu matakin al'umma domin yin aikin gayya akan wasu matsalolin; a yayinda wasu kuwa sai Gwamnati ta kawo dauki domin gudanar da ayyukan.
A irin wannan matakine al'ummar Sabuwar low cost da bayan Gidan Taki da malali suka dauka domin yin aikin gayya tareda tallafin wasu masu karfi a cikinsu domin gyaran magudanan ruwa a wadannan unguwanni domin magance barazanar rugujwar gidaje da zaizayar kasa da ambaliyar ruwa ke jaza musu a kowace shekara, musamman a lokutan damina.
Saidai kamar yadda aka fadi a baya, wasu matsalolin sunfi karfin dai-dai-kun al'umma ko matakin aikin gayya, ma'ana girman matsalolin saidai Gwamnati "ikon Allah".
Wannan daliline yasa wadannan al'umma ke kara roko ga Gwamnatin mal Dikko Radda data kawo daukinta na gaggawa ga wannan al'umma kafin matslar ta kara ta'azzara, kasantuwar zaizayar kasar na cigaba da tilasta ma wasu mazauna Unguwannin gudun hijira, Kamar yadda suka bayyana, unguwanni sunsamu nakasu kwarai ta fuskokin rayuwa sakamakon wannan matsala, kama daga kasuwanci, Neman ilmi, lafiya da sauran muhimman bangarori na rayuwa.
A saboda haka ne, suke da kyakkyawan fatan wannan Gwamnati zata share musu hawaye ta hanyar amsa wannan roko da suka jima sunayi a lokuta mabanbanta.