Muhimmancin da Hanyoyin Ruwa ke da su ga Muhalli
- Katsina City News
- 10 Jun, 2024
- 527
Samar da wadatattun hanyoyin ruwa da magudanai na daga ayyukan da gwamnatoci a matakai daban-daban ke aiwatarwa domin kyautata rayuwar al'ummomin alkaryu da kauyuka da birane.
Har ila yau harkar koyo da koyarwa da habbakar tattalin arziki na iya samun naqasu da koma baya idan babu hanyoyi ingantattu nayin kai-da-komowa a cikin al'umma.
Alal misali, kafin Aiwatar da ayyukan magudanan ruwa da kwalbatoci karkashin shirin NEWMAP Wanda yanzu Ya koma ACRESAL, an samu matsaloin asarar rayuka da dukiyoyi a bangarori da dama na jihar Katsina, sakamakon ambaliyar ruwa da rashin isassun hanyoyin ruwa.
Amma da yanzu tasirin wadannan ayyuka na tsanyoyi ,misali a kofar Guga zuwa Tudun yanlihidda zuwa Kofar Sauri ba boyayyen Abu bane ga al'ummar Jihar Katsina, yanzu yaushe rabon aji labarin ambaliar ruwa ko asarar dukiya a wannan unguwanni da makamantansu.
Abisa lura da irin tasirin irin wadannan ayyuka da makamantansu da Gwamnati ta aiwatar, al-ummomin Sabuwar Dustin safe low cost har yazuwa malali ke kara roko ga Gwamnatn jihar Katsina data sama masu hanyoyin ruwa a wadannan unguwanni, kafin matsalar ta kara ta'azzara, musamman wannan yanayi na damina.
Samarda wadannan magudanan ruwa ba karamin tasirin zaiyiba wajen inganta walwala da zamantakewar wadannan al-ummomi, musamman ta fuskar Tattalin arziki da Neman ilimi.
Haka kuma, mazauna wadannan unguwanni sun aiwatarda wasu ayyuka da basufi karfin aljihunsu ba, tare da taimakon wasu masu hali a cikin su, duk da wannan yanayi da ake ciki na matsin tattalin arziki ,amma girman wannan matsala tasa dole sai Gwamnati tashiga lamarin.
Da hakane, wadannan al-umma ke kara nanata goyon bayansu ga shirye-shirye da tsare-tsare na Gwamnati tareda nusar da Gwamnati irin matsalolin da suke fuskanta sakamakon rashin hanyoyin ruwa wadatattu.