Wayar Hannu Ta Farko A Najeriya 2021
- Katsina City News
- 09 Jun, 2024
- 493
A Rana Mai Kamar Ta Yau 9 ga watan Yuni 2021 Otunba Niyi Adebayo ya gabatarwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wayar hannu ta farko da aka yi a Najeriya.
An gabatar da wayar ne a yayin taron Majalisar zartarwa ta Tarayya (FEC) wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
Bugu da ƙari, a taron, shugaban kasar ya rantsar da kwamishinonin tarayya na Hukumar Kula da Yawan Jama'a (NPC) da Hukumar Kula da ma’aikatan Tarayya (FCSC).
Hadimin shugaban kasar a kafofin watsa labarai na zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana hakan a cikin wani wallafa da yayi a shafinsa na Facebook.
A Ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, 2021, Hotuna da rahotanni su ka Cika Kafafen Yada Labarai Cewa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) Ya Gabatar wayar farko (Smartphone) da aka Kera a Najeriya da aka fi sani da ITF.
Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Otunba Niyi Adebayo, yayin da yake gabatar da wayoyin ga shugaban kasa gabanin taron zartaswar tarayya ya sanya ta a matsayin ta farko da ta taba fitowa daga kasar.