TATSUNIYA TA (24) LABARIN KUREGE DA KURA NA BIYU
- Katsina City News
- 07 Jun, 2024
- 336
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Kurege yana farauta a daji sai ya ga mushewar Kurciya, sai ya dauka ya ajiye a kan itace. Ya ci gaba da tafiya sai kuma ya ga mushewar Giwa. Ya matsa kusa, ya dubi mushewar da kyau, ya yi dariya. Daga nan sai ya kai wa Kura ziyara. Ya same ta tana saka zana sai ya ce: "Ki bari in kwanta a kan zanar nan taki." Sai Kura ta ce: "To, kwanta mana."
Da Kurege ya kwanta sai ya lumshe idanunsa. Jim kadan kuma ya bude: sai ya ce da Kura: "Na yi mafarki wai mun je yawo da ke sai muka sami kan Kurciya mai kyau." Kura na jin haka sai ta ce: "Kai-kai, ai gara ka sake kwanciya ko ka kara yi mana mafarki mai dadi fiye da wannan." Kurege ya rufe ido, ya bude sai ya ce: "Kai na sake yin mafarki wai kin sami mushewar Giwa ke kadai." Kura na jin haka sai ta ce da Kurege: "To mu tafi mu bi sawu."
Da ya ji sai ya ce: "Yanzu dare ya yi, sai dai can idan gari ya kusa wayewa." Bayan zakara ya yi cara sai Kura ta sake cewa da Kurege su tafi, shi ko ya ce ta bari sai da hantsi. Kura ta kasa hakura. Sai ta hura wuta a kan dakinta wai hantsi ke nan. Amma Kurege sai ya gane, ya ce da ita: “Ai wannan wuta ce kika hura a kan dakinki."
Daga karshe dai da gari ya waye hantsi ya daga, sai suka kama hanyar hin sawun mafarki. Suna cikin tafiya sai Kurege ya tura Kura wajen kan Kurciya. Da ta gani ta kirawo shi suka raba. Suna cikin tafiya sai Kurege ya tura ta wajen mushewar Giwa. Da ta gani ta yi kashi domin ta kasayar da abin da ke cikinta, domin ta sami damar cin naman mushewar Giwa sosai, tun da ga nama kamar ba iyaka. Kurege da Kura suka shiga gyara nama. Suna cikin wannan aiki ke nan sai ga 'ya'yan Giwa sun bi sawun uwarsu. Sai tsoro ya kama Kurege da Kura. Sai Kurege ya ce: "Zan shiga cikinta in buya," Sai Kura ta ce: "Kai yaro ne, ni babba ce zan shiga ciki."
Da Kura ta dage sai ta shiga cikin Giwa, shi sai ya shiga mafitsarar mushewar Giwar. Da 'ya'yan Giwa suka je kan mushewar uwarsu, sai suka fitar da mafitsarar suka yar da Kurege a ciki. Da Kurege ya fita daga cikin mafitsarar, sai ya ga wata karama daga cikin 'ya'yan Giwar tana yankan ciyawa sai ya ce: "Wayyo, wa ye ya zuba mini ruwa?" Sai 'ya'yan suka ce: "Ayya sannu ba mu san kana nan ba." Sai ya ce: “A'a, me ya sami kakata?" Sai baki dayansu suka ce: "Ba mu sani ba."
Sai Kurege ya ce: "Ku kawo jar dawa in zuba a ruwa in yi muku duba." Da suka ba shi jar dawa sai ya ce: “Abin da ya kashe kakar nan tawa yana cikinta. Abin da za ku yi sai ku dauko sanduna ku yi ta dukan cikinta." Sai ko 'ya'yan Giwa suka yi kamar yadda Kurege ya fada. Da duka ya ishi Kura sai ta ce: "Ba ni kadai ba ce, ni da Kurege ne."
Kurege ya ce: "Kada ku saurari maganarta, ku bugi wajen gefen bakinta." Haka suka yi ta jibgar Kura, ta fito daga cikin Giwa jina-jina, ta gudu ta tsira da kyar. Sai 'ya'yan Giwa suka dauki sauran mushewar uwarsu suka kai gida domin su binne. Sai Kurege ya roki su ba shi kan kakarsa domin wai ya binne a gidansa. Sai suka yarda suka ba shi. Niyyarsa yana so ya dafa ne. Da zuwansa gida sai ya sa a tukunya aka hura wuta, aka sa tukunya a kan wuta, kuma ya ce wa 'yarsa: "In wuta ta mutu sai ki zo ki fada mini cewa ciyawa ta kare a gaban doki."
'Yar Kurege ta ce: "To baba, na ji." Shi kuwa Kurege ya sa kai ya koma wurin 'ya'yan Giwa zaman makoki. Da wuta ta cinye icen, sai 'yar ta je gidan Giwa inda ubanta ke zaman makoki ta ce masa: "Baba ciyawa ta kare a gaban doki."
Kurege na jin haka ya dauki hannu, kuma ya tashi ya bi 'yarsa suka tafi gida. Ya tarar naman kan Giwa bai gama dahuwa ba, sai ya kara ice, ya koma gidan makoki. Bayan wani dan lokaci da kan Giwa ya gama bararraka, sai yarinyar ta koma gidan Giwa inda ake zaman makoki ta ce masa: "Baba ai kan kaka kamar ya nuna."
Da 'ya'yan Giwa suka ji haka, sai suka ce: "Ashe ba binne kan ka yi ba dafawa kake yi? To sai a kama shi a kashe nan take." Da ya ji haka sai ya falle da gudu tal-tal-tal ana bin sa, sai ya tarar da wani Kuregen yana saka. Sai Kurege mai saka ya ce da Kurege mai gudu: "Me ya koro ka?"
Sai Kurege mai gudu ya ce da Kurege mai saka: “Ai Sarki ne ke son wutsiyar Kurege dubu, sai mu gudu." Da jin haka sai Kurege mai saka ya falle da gudu shi kuwa Kurege mai laifi ya yi zamansa ya kama saka.
Da 'ya'yan Giwa da masu taya su bin sawun Kurege mai laifi suka ga wancan Kurege yana gudu, sai suka bi shi, har suka kama shi, suka kashe. Kurunkus.
Mun ciro wannan Labarin daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman