Harin 'Yan Bindiga a Dutsinma: Fiye da Mutum 30 Sun Mutu, da Dama Sun Jikkata
- Katsina City News
- 06 Jun, 2024
- 904
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Fiye da mutum talatin ne suka rasa rayukansu yayin da wasu ke kwance a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya a Katsina don samun kulawar likitoci, sakamakon hare-haren 'yan bindiga a kauyukan Dutsinma da Safana.
A ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024, maharan da suka kai kimanin babura 150, kamar yadda shaidu suka tabbatar wa Jaridar Katsina Times, sun kai mummunan hari a kauyukan Dutsinma da Safana. Sun kashe fiye da mutum 40 tare da jikkata da dama, sannan sun kwashe dukiyoyin mazauna yankin.
Maharan da ake kyautata zaton sun kai su dari uku sun farmaki kauyukan Tashar Kawai Mai Zurfi, Sabon Gari Unguwar Banza, Dogon Ruwa, Sanawar Kurecen Dutsi, Unguwar Bera, Kuricin Kulawa, Larabar Tashar Mangoro, Sabaru, Ashata, da wasu kauyukan karamar hukumar Safana da suka hada da Unguwar Ido, Kanbiri, Kunamawar Mai Awaki, Kunamawar 'Yargandu. Haka zalika, a ranar Laraba da wayewar garin Alhamis, sun sake komawa kauyukan Dogon Ruwa, 'Yar Kuka, Rimi, Lezumawa, da sauran kauyukan da ke kusa da garin Safana kan iyaka da Dutsinma.
A halin da ake ciki, mazauna yankunan fiye da kauyuka 15 sun baro gidajensu, wasu suna garin Dutsinma, wasu kuma suna kauyen Turare don samun mafaka daga barazanar maharan.
Wasu da abin ya shafa sun shaida wa Katsina Times cewa suna tsaka da neman gawarwaki don suturtasu a bisne, suka sake ganin maharan sun fito amma ba a san inda suka nufa ba.
Game da lamarin, mun nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Katsina, amma ba mu samu wani karin bayani ba zuwa hada wannan rahoto.
Hare-haren 'yan bindiga na kara tsananta a wasu yankunan Jihar Katsina, inda ko a makon da ya gabata aka samu hare-haren a yankunan Batsari, Kankara, da Faskari.
A wannan makon, Ministan Tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar, ya ziyarci Jihar Katsina inda ya kai wa barikoki da hedikwatar sojojin Briget 17 ziyarar karfafawa dangane da nasarorin da rundunar sojojin ke samu. Haka zalika, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa a fafatawa da 'yan ta'adda a jihar an samu nasara da kaso 70 cikin dari.