AL'UMMAR WASU UNGUWANNI A JIHAR KATSINA NA NEMAN DAUKIN GWAMNATIN JIHA
- Katsina City News
- 06 Jun, 2024
- 391
Al'ummomin sabuwar Dutsin-tsafe low cost dana bayan filin sukuwa da gidan taki a cikin birnin kastina sunyi roko ga gwamnatin jihar Kastina data Kawo musu DAUKIN gaugawa a yankin don ceto su daga barazanar shafewa kwanta Kwara ta hanyar Gina musu babbar hanyar ruwa.
Al'ummar wadannan unguwa sunyi wannan rokone a lokacin da suka fita GABA dayan su don zagayawa tare da duba irin barna da barazanar da wata babbar hanyar ruwa da ta biyo ta cikin UNGUWANNIN ke yi ga gidajen su, in da Kuma daga bisani suka gayyaci Yan jarida domin su gane ma idon su girman matsalar.
Kasantuwar mazauna yankin sun hade kan su waje Daya domin tunkarar matsalar hanyar zuwan Ruwan gadan gadan ne ya Basu damar aiwatar da wani aikin gayya na samar da yar karamar hanyar ruwa a wannan yanki.
Da yake a madadin mazauna yankin, Mal. Zahradeen SaninZakka ya bayyana cewa wannan matsala ta jima tana cimusu tuwo a kwarya wadda tana barazana matuqa ga rayuka da dukiyoyin mazauna wannan unguwanni.
Ya qara da cewa wannan ruwa suna gangarowane daga titin Ring road ya biyo ta filin sukuwa,zuwa sabuwar lowcost ya gangaro malali ya bulle Gadar Sani Danlami, Mal. Zahradeen ya Kuma Kara da cewa wannan ruwa ya zaizaye mafi akasarin gidajen dake wannan yanki, inda wasu dayawa daga ciki suka kaurace ma wannan yanki don tsira da rayuka da dukiyoyinsu.
Har ila yau, wannan matsala na Neman durkusar da harkar kasuwa da lafiya da Neman ilimi na mazauna wadannan unguwanni, kasancewar dukan wadannan abubuwa sun ta-allaka ne da samun kyakkyawar hanya da kuma kwanciyar hankali.
A saboda haka dukan wadannna unguwanni da wannan ruwa yakebi, suna cikin hali na fargaba da rashin tabbas, musamman a lokutan Damina.
Don haka, roqo ga Adalin Gwamna, Mal Dikko Radda da ya kawo musu Dauki na gaugawa ta hanyar sama musu mafita daga wannan hali.
Haka kuma sunyi addu'ar karin samun nasarar zaman lafiya da yalwar arkizi a jihar katsina da tarayyar Nigeria.