ƁARAYIN DAJI NA KAI ZAFAFAN HARE-HARE A YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 04 Jun, 2024
- 450
Misbahu Ahmad @ Katsina Times
Ɓarayin daji na kai zafafan hare-hare a yankunan ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina, inda suka kashe a ƙalla mutane goma cikin ƙasa da mako biyu.
A ranar laraba 22-05-2024, sunkai hari da dare a ƙauyen Kagadama (Tashar'icce), inda suka kashe mutane biyu, sannan suka yi garkuwa da mutane huɗu, miji da mata da wasu mutum biyu, sannan sun sace shanun huɗa guda goma sha biyu.
Sai ranar alhamis 23-05-2024, inda suka kashe wani bawan Allah mai suna Malam Muntari a ƙauyen Batsarin'alhaji lokacin da yaje ɗibar ruwa a rijiyar dake gab da ƙauyen, lamarin ya faru da misalin 11:00am na ranar.
A ranar lahadi 26-05-2024 da dare sunkai hari ƙauyen Tudunraha, inda suka bindige mutane biyu, sannan sukayi awon gaba da mata huɗu.
A ƙauyen Nasarawa ma sunkai hari da daren ranar laraba 29-05-2024, kuma sun kashe mutum ɗaya nan take, sun jikkata ɗaya, sanan sun bi ta ƙauyen Tudawa sun ɗauki mata shida.
Sun sake kai hari ƙauyen Batsarin'alhaji a ranar alhamis 30-05-2024, inda suka rutsa da wani bawan Allah yana aiki a gonarsa dake kusa da ƙauyen suka kashe shi.
Ɓarayin na daji masu satar dabbobi da garkuwa da mutane da kisa ba dalili, sunkai wani mummunan hari a ƙauyen Gajenharo cikin daren ranar lahadi 02-06-2024, inda suka kashe mutane ukku sannan suka yi ƙone-ƙonen gidaje tare da sace-sace dukiya.
Katsina Times
www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762