Kungiyar AFAN Ta Jinjinawa Gwamna Raɗɗa Akan Taimakon Da Ya yi Wa Manoma A Jihar Katsina
- Katsina City News
- 31 May, 2024
- 682
Shugaban kungiyar Manoma ta ƙasa reshen jihar Katsina AFAN Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya jinjinawa gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa akan taimakon takin zamani tan 20,000 da yi wa Manoma domin bunƙasa noama a jihar.
Hakan yana kunshe ne acikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar sannan aka rabawa manema labarai a Katsina inda ya ce raban da gwamnati ta sayo takin zamani a rabawa jama'a bana shekara bakwai ke nan
Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo wanda ya yaba da irin ƙoƙarin gwamna Dikko Raɗɗa bisa raba machina guda 722 tare da magungunan ƙwari ga sabbin ma'aikatan gona 722 da ya ɗauka aiki domin su ilimantar da manoma dabarun noma na zamani a faɗin mazaɓo 361 da ake da su a jihar Katsina
"Wannan gudunmawa na da nufin ƙara farfaɗo da harkokin noma da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya kudiri aniyar wanda daman anan fanni yake da kwarewa." Inji Gwajo-gwajo
Kazalika ya bayyana cewa manoma a jihar Katsina su kwana da shirin samun wasu gudunmawar da ta haɗa da kayayyakin noma ta hanyar yin amfani da tsarin gwamnatin jihar na bunƙasa harkokin noma a jihar.
A cewar sa, tunda Nijeriya ta dawo turbar dimokuraɗiyyar babu gwamnan da ya raba takin zamani a jihar Katsina kamar Malam Dikko Umar Raɗɗa.
Shugaban kungiyar Manoma ta AFAN Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya yi kira ga manoma a jihar Katsina da su yi amfani da wannan takin wajen noma abinci tare da karfafa su da su cigaba da yi wa jihar Katsina da ƙasa baƙi ɗaya addu'o'in samun zaman lafiya.