Shugabannin jam'iyyar APC sun bukaci hadin kai da sulhu a na 'ya'yan Jam'iyyar a jihar Katsina
- Katsina City News
- 26 May, 2024
- 504
"Ku yi hakuri ga magoya bayanmu na jam'iyyar APC musamman wadanda suka tsaya takarar shugabancin kananan hukumomi amma ba su yi nasara ba," in ji Bala Abu Musawa
A ranar Alhamis, 24 ga watan Mayu, da juma'a 25, ga watan, 2024 Bala Abu Musawa ya da tawagar gwamnatin jihar Katsina suka cigaba da zagaye kananan hukumomi na jihar don neman hadin kai ga 'ya'yan Jam'iyyar APC.
Makasudin rangadin dai shi ne ganawa da shugabannin jam’iyyar a matakin kananan hukumomi da mazabu, da sauran shuwagabannin jam’iyyar, domin warware duk wani rikici ko korafe-korafe da ya taso a zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Tawagar ta ziyarci kananan hukumomin Batsari, Jibia, Kaita, Rimi, da Charanchi, Kaita, Kurfi Dutsinma, Batagarawa da Rimi, Da yake gabatar da jawabin sa, jagoran rangadin, Bala Abu Musawa, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina ta kafa kwamitin tare da hadin gwiwar jam’iyyar APC na jihar domin sasanta dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina.
Musawa ya jaddada cewa, “An kafa wannan kwamiti ne domin magance korafe-korafen da suka biyo bayan zabukan fidda gwani na kananan hukumomi da kansiloli, yace "mun fahimci cewa wasu ‘ya’yan jam’iyya na cikin bacin rai da fushi, shi ya sa muke umurtar shugabannin jam’iyyar da ‘yan takara da su nemi sulhu, su nemi afuwar wadanda suka yiwa ba daidai ba". Yace kowa na da irin gudunmawar da zai bada don haka babu wanda ba namu ba kowa namu ne indaina jam'iyyar ya fito."
‘Yan takarar kananan hukumomin sun ba da tabbacin bin wannan umarni, da nufin hada kan jam’iyyar APC tare da yin aiki tare domin samun nasarar ta.
Tawagar ta hada da mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa, Hon. Yau Umar Gwajo Gwajo, Alhaji Sabo Musa, mai taimakawa gwamnan jihar Katsina a kan wayar da kan jama'a, tare da shugabannin jam'iyyar jiha da na yanki.