RA'AYI: Alaƙanta Taron Tsoffin Gwamnonin APC Na Zamfara Da Matsalar Tsaro, Alamu Ne Na Yaudara
- Katsina City News
- 22 May, 2024
- 514
Daga Jibo Magayaki Jamilu PhD (fcism, fcipdm, fpmc)
Na karanta wani abin takaci a wata sanarwar manema labarai da Sakataren yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, wanda ya fitar dangane da taron tsofaffin gwamnonin huɗu da suka gudanar a kwanakin baya.
A wani mataki da ake ganin ya na da alaƙa da siyasa, gwamnonin sun yi yunƙurin Alaƙanta taron nasu da matsalar tsaro, inda suke wasa da hankalin jama’a, tare da kawar da hankalin su daga ainihin manufar su.
Ya kamata a lura da cewa taron na siyasa ne kawai, kuma ba shi da wata alaƙa da magance wahalhalun da talakawa ke fuskanta ko kuma ta fuskar tsaro na gaskiya a jihar, ta hanyar yin yunƙurin samar da labarin cewa tattaunawar tasu ta ta'allaƙa ne kan lamuran tsaro, wanda sam ba haka ba ne.
Tsoffin gwamnonin sun shiga wani salo da nufin rufe muradun su na siyasa, tare da kawar da hankalin 'yan Zamfara daga rawar da suke iya takawa a halin da ake ciki.
A halin yanzu dai al’ummar Zamfara na fuskantar matsanancin ƙalubalen tsaro da ke buƙatar kulawa ta gaggawa.
Sai dai a maimakon tunkarar waɗannan matsalolin da ke damun su, Tsoffin gwamnonin sun gwammace su ba da fifikon wajen siyasar su.
Wannan wani abu ne mai ban-takaici na nuna son kai, wanda ke nuna rashin nuna damuwa ga walwala da lafiyar al'ummar Zamfara.
Yana da matuƙar muhimmanci jama'a su fahimci wannan yaudara da neman a yi musu hisabi daga tsoffin shugabannin su.
Ƙoƙarin inganta tsaro da rage wahalhalun da jama'a ke fama da shi, ba za a iya samu ta hanyar wasa da hankalin jama'a da sunan siyasa ba.
Dole ne Tsoffin Gwamnonin su fahimci cewa ba a manta da abin da suka aikata ba. Kamata ya yi da su fifita ainihin buƙatun talakawa, musamman samar da tsaro, sama da buƙatun su na siyasa.
Duk da cewa waɗannan tsoffin gwamnonin da ake gani, su ne musabbabin duk rikicin da ake fama da shi, saboda rashin kula da halin da al’umma ke ciki a baya, ba su taɓa neman haɗuwa, ko haɗa kai da Gwamna Dauda Lawal don samar da mafitar jihar ba.
Rashin yin wani hoɓɓasa wajen ganin an shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar Zamfara, wani babban abin tunawa n, inda suka na son-kai da kuma rashin jajircewar su wajen kyautata rayuwar al’ummar Zamfara.
Gwamna Dauda Lawal ya na namijin ƙokari wajen ganin an samar da zaman lafiya da tsaro a Zamfara, wacce ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Yunƙurin sa a wannan fanni, ya haɗa da yadda ya haɗa kai da jami’an tsaro na cikin gida, da hukumomin tsaro, da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin samar da zaman lafiya. Sannan ga Askarawan Zamfara da ya kafa.
Duk da wannan ƙoƙari na Gwamna Dauda Lawal, wannan taro na tsaffin gwamnonin da ake ganin an shirya shi ne don siyasa, ya nuna rashin mutunta irin ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na ganin an magance matsalar rashin tsaro.
Al’ummar Zamfara sun cancanci shugabanni masu sadaukar da kai wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar, kamar dai irin Dauda Lawal, maimakon masu neman yin amfani da son kan su.
Rashin goyon bayan ƙoƙarin da Gwamna Dauda Lawal ke yi na kawo ƙarshen tashe-tashen hankula a Zamfara, wanda waɗannan tsaffin gwamnonin suka yi, ba wai kawai abin takaici ba ne, har ma ya nuna rashin jajircewarsu wajen neman ci gaban jihar.
Lokaci ya yi da jam’iyyar APC da tsaffin Gwamnonin ta za su fifita rayuwar al’ummar Zamfara fiye da buƙatun kan su na siyasa, kamar yadda wannan taron dai bai wuce taron siyasa da nufin biyan buƙatun kan su ba. Sannan kuma yunƙurin alaƙanta shi da matsalar tsaro, bai wuce yaudara ba.
Jibo, ya rubuto ne daga Gusau