TSOHON GWAMNA SHEMA: KA RIKE GIRMAN KA
- Katsina City News
- 17 May, 2024
- 535
...Nazarin jaridun KATSINA TIMES da TASKAR LABARAI
Mun saurari wata hira da gidan Rediyon BBC ya yi da tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema. Hirar da aka fara tsakure, za a sa cikakkiyarta gobe Asabar 18/05/2024.
Wata magana da tsohon gwamnan ya yi a kan aikin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, Shema bai yi wa kansa adalci ba, kamar yadda bai yi wa gwamnatin Masari da al'ummar jihar Katsina adalci ba.
Na daya. Kila tsohon gwamna Shema ya manta, amma bari mu tuna masa. Daga aikin karshen gwamnatin Masari ita ce, shi ne amincewa da gwamnatinsa ta yi na a sulhunta tuhumar da Hukumar da ke yaki da cin hancin da rashawa (EFCC) ke yi wa tsohon gwamnan a gaban kotuna daban-daban.
Daya daga cikin tuhum-tuhuken da ake yi masa a kan kudaden kananan hukumomi a babbar kotun jahar, an kusa kai karshe, Alkalin ya yi mutuwar 'fuj'a'.
Dayar kuma a kan kudin tallafin SURE-P ne, wanda ake yi a Babbar Kotun Tarayya da ke Katsina.
Dukkanin shari'un nan sun kunshi dubban miliyoyin Nairori na mutanen Katsina.
Ana shari'ar, shaidu da hujjoji na bayyana aka tsaida ta saboda dattaku da maslahar jihar Katsina.
Gwamnatin Masari ce ta yi wannan.
Na biyu: A 2015 gwamnatin Masari ta iske bashin wadanda suka mutu da wadanda suka ajiye aiki a jihar Katsina na shekaru. Gwamnatin Masari ce ta samo kudi sama da biliyan 10 a wancan lokacin duk ta biya su. Wa ya bar bashin? Gwamnatin Shema. Wa ya biya? Gwamnatin Masari.
Na uku. Shema ya halarci bikin bude aikin gadar sama wadda aka yi a unguwar GRA da ke Katsina. Ginin da ya sanya jihar Katsina cikin sahun masu gadar sama don hana cinkoso da kuma kawata gari. Wa ya yi gadar? Gwamnatin Masari.
Ibrahim Shema da shi aka yi bikin bude ta a watan Maris, 2023.
Na hudu. Wa ya gina gadar kasa ta Kofar Kaura? Tsakanin Shema da Allah bai san da ita ba, kuma bai taba bin ta ba?
Gadar ta taimaka wajen kawata gari da kuma hana cinkoso a wannan yankin? Wa ya yi ta? Gwamnatin Masari.
Na biyar. Wa ya yi gadar Kofar Kwaya? Kofar da ta hada duk manyan makarantun Katsina da cikin gari da kasuwannin garin da kuma tashoshi, ta hada hanyar Katsina da zuwa Maradi da ke kasar Nijar.
Don Allah shema bai san da ita ba?
Na shida. Katafaren ginin Hukumar Tattara Haraji ta jihar Katsina da ke kan titin zuwa Kano, wa ya yi shi? Suka taso daga wani dan akurki, suka komo ginin da ko'ina abin nunawa ne.
Ko in hanya ta kawo Shema zai wuce wajen, rimtse idanunsa yake tun da aikin na kan babbar hanya ne da ta hada Katsina da Kano?
Na bakwai. Wa ya yi hanyar ruwan da ta taso daga Kofar Guga ta ratso har zuwa babbar hanyar ruwa da ke 'Yar Kutungu?
Hanyar ruwa ce da tsawon shekaru ke yi wa unguwani barazana, amma Masari ya kawo karshen wannan annoba ta shekara da shekaru. Kila Shema bai san wannan ba domin ya shafi unguwanin talakawa ne?
Na takwas. Babban asibitin Katsina mai tsohon Tarihi na talakawa ne. Har gwamnatin Shema ta gama mulki ba ta kashe masa Naira milyan 100 ba. Ya gwamnatin Masari ta canza masa fasali? Wa ya yi aikin? Masari ko Shema?
Na tara. Dam din Ajiwa. Tunda aka kafa shi, wa ya yi masa gyara?
Gwamnatin Masari ce ta canza masa fasali zuwa na zamani. Wane aiki gwamnatin Shema ta yi wa dam din Ajiwa?
10.Wa ya gina gidaje a kusa da asibitin gwamnatin Tarayya da ke Katsina? Kodayake ba dole ba ne Shema ya sani, don asibitin na talakawa ne. Kila hanya ba ta taba bi da shi ba domin hanyar unguwar talakawa ce.
11.Wa ya gina hanyar ruwa ta garin Jibia wadda ke ci wa jama'ar yankin tuwo a kwarya saboda barnar da ruwa ke masu duk shekara?
12.Wa ya gina hanyar Sandamu zuwa Baure?Kafur zuwa Mahuta? Gora zuwa Makauraci? Da sauran hanyoyi a duk fadin Katsina? Gwamnatin Masari.
13.Wa ya gyara gidan Gwamnatin Jihar Katsina da ake kira Katsina House da ke Abuja?
Wannan gidan yanzu ya zamar wa jihar Katsina wata babbar kadara, kuma kafar samun kudin shiga. Gwamnatin Masari ce ta yi aikin gyara shi.
15. Wa ya Gina Dam din Danja, Dam mafi girma a yankin funtua .Wanda za a sha kuma za ayi noman Rana.Gwamnatin Masari.
16, wa ya Gina tsangayar karatun aikin Gona na jami ar umaru Musa yar adua dake layin minista? Ginin dashi kanshi banda matsalar tsaron yankin yana iya zama jami a mai zaman kanta
18, wa ya farfado da darajar makarantun firamare da sakandare na karkara? Lokacin da Masari yazo akwai makarantun da tunda aka Gina su zaman balarabe Musa da lawal kaita ba a taba su ba, sai zuwan gwamnatin Masari
19.Wannan dan kadan ne daga ayyukan Masari wanda Shema ya ki yi wa adalci.
20,.Nawa Shema ya amsa daga gwamnatin Tarayya a shekaru takwas? Nawa Masari ya amsa?
21,.Abin da gwamnatin Shema ta amsa daga gwamnatin Tarayya da hukumomin kudi daban-daban a shekaru uku, ya fi abin da gwamnatin Masari ta amsa a shekaru takwas baki daya da ta yi.
22,.Don haka bai dace ba, kuma ba girman Shema ba ne ya fito a kafar yada labarai kamar BBC yana yin shagube da gugar zana ga gwamnatin da ta tallabe shi.
23.Mu a Katsina muna bukatar manyan mu su zama masu dattaku da girmama juna.
Shawara: shema ka rike girman ka.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762
Email. newsthelinks@gmail.com