AMIRUL HAJJI NA KATSINA YA DAKATAR DA BA MAHAJJATA BABBAR JAKA MAI 32KG. ..........Ya kuma kafa Kwamitin bincike
- Katsina City News
- 14 May, 2024
- 579
Muazu Hassan
@ Katsina Times
Alhaji Tukur Ahmad jikamshi tsohon mataimakin gwamnan Katsina kuma Amirul hajj na aikin hajjin wannan shekarar ya dakatar da baiwa mahajjata babbar jaka mai nauyin 32kg.ya kuma kafa Kwamitin bincike karkashin mai Shari a Bawale, akan a binciki me ya kawo dan kwangilar ya Saba kaidar kwangilar da aka bashi ta ya kawo karamar jaka mai 8kg a Katsina ya kai babbar jaka a kasar Makka don a baiwa alhazai.
Wannan umurnin ya zo ne, a zaman da Amirul hajj da yan tawagarshi yayi da hukumar alhazai a yau talata 14/5/2024 a dakin taro na hukumar alhazan Katsina.
A wajen taron aka kawo cewa Dan kwangilar jikkuna ya Saba yadda aka sabayi tsawon shekaru. Inda a tsarin kwangilar a kuma kudin da aka biya shi zai kai jikkuna masu 32kg a makka.
Nan wasu suka nuna irin yadda za a wahalar da alhazan in aka basu babbar jaka tun daga Najeriya, ana ma iya samun matsala da kamfanonin jiragen sama Wanda daga nan za a jawo alhazan su fara zagin gwamnatin, alhali ba laifin ta bane.
Jaridun Katsina Times sun lura dan kwangilar ya na neman rarar wasu kudi ne da suka shafi na kai kayan makka da ajiye su da kuma kai ma mahajjata jikkunan su har gidajen su a Makka, wadannan rarar kudin, Ko dan kwangilar shi kadai zai amfana? Ko ko za'a maido ma alhazai kudin su ne? Ko hukumar alhazai ta jaha?
Amsar da shugaban hukumar alhazan jahar Katsina yaki bamu kenan da muka Kira shi a waya don neman Bahasin labarin.
A zaman na yau amirul hajj ya kewaya ginin na hukumar alhazan ya kuma nuna bacin ranshi ga duk inda yaga anyi ba dai dai ba. Ya kuma bada umurnin a gyara da gaggawa.
Gobe laraba za a yi zama na masu ruwa da tsaki a hukumar alhazan ta jahar Katsina akan aikin hajjin na bana 2024.