'Yan Siyasa ne kaɗai da Iyalansu ke jin Dadi a Nijeriya. -NLC
- Katsina City News
- 14 May, 2024
- 566
“Banda 'Yansiyasa da iyalansu babu mai jin daɗi a Najeriya -inji Shugaban NLC a Katsina
Daga shafin Katsina post
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Katsina Comrade Husaini Hamisu 'Yanduna, shi ne ya bayyana haka a lokacin da suke gudanar da gangamin ƙin amincewa da ƙarin kuɗin wutar lantarki a Najeriya.
Comrade Dr. Husaini Hamisu 'Yanduna, ya ce kamata ya yi ace hukumar sun kira masu ruwa da tsaki a ƙasar nan kafin su ƙara ma wutar lantarki kuɗi, amma bai kamata ace su kaɗai za su yanke hukuncin ba a wannan lokacin da ake ciki, wanda kuma ita kanta wutar ba su bada ta na tsawon awa 12 ko 24 a rana.
Ta dalilin haka ne bi sa umurnin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, reshen jihar Katsina ta rufe kamfanin bada hasken wutar lantarki (KEDCO) da kuma hukumar kula da rarraba wutar lantarki dake jihar sakamakon ƙarin kuɗin wutar lantarkin ba bisa ƙa'ida ba.
Ƙungiyar NLC da TUC na ƙasa reshen jihar Katsina suka jagoranci rufe ofisoshin a wata zanga-zangar lumana da su ka gudanar a safiyar ranar Litinin 13 ga watan Mayu, 2024.
Lokacin gangamin akwai tawagar shugaban TUC, Alh. Muntari Abdu Ruma, shugaban ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar Katsina Comrade Nasiru Wada Mai'adua, Comr. Buhari Rafukka, da 'ya'yan ƙungiyar da sauransu.
Shugaban ya nanata cewa, halin da ake ciki na matsalar tattalin arziki ƙasa da ake ciki, bai kamata ba a ƙara kuɗin wuta a Najeriya, an cire tallafin Mai gashi yanzu ma an cire tallafin NEPA, yace ya talaka zai yi ya ji daɗi a Najeriya.
Ya ƙara da cewa, a Najeriya ne kaɗai al'ummar unguwa za su je su siyo fol da wayar wuta da kuɗaɗen su, wasu ma har da haɗa kuɗi a sayi taransifoma, amma bayan sun sanya na ɗan wani lokaci ba na su ba ne zai zama na hukumar wutar lantarki saboda son zuciya.
Saide, kafin haɗa wannan rahoton mun so jin ta bakin shugabannin hukumar wutar lantarki a jihar amma ofishin su a rufe, haka kuma bamu samu jin ta bakin su a wayoyoyin salula ba. Amma ko bayan wallafa wannan rahoton zamu tattauna da su idan muka same su a wayoyoyin su.