Zaben kananan hukumomi: "Murɗiya akai mana ba sasanci ba" inji 'Yan takarar APC a Dutsi
- Katsina City News
- 11 May, 2024
- 838
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Masu Neman muƙaman shugaban karamar hukumar Dutsi da Kansiloli sun koka akan rashin Adalci da murɗiya da suka ce an yi masu.
Sun bayyana zargin nasu karara akan Shugabana jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar ta Dutsi, inda suka ce ya ma ki yadda a zauna balle ayi sasanci kawai sai suka ji ance wai anyi sasanci kuma wai har an fidda Dantakara.
Ibrahim Sirika Abubakar daya daga cikin 'yan takarar shugabacin karamar hukumar ta Dutsi yace; "Ance wai Mai girma tsohon minista Hadi Sirika shine yace ga wanda ya ke so kuma ya aiko yace a bashi dole shi za'ayi, mu kuma muna ganin a dalci irin na mai girma Minista ba zai yiwa al'ummar Dutsi haka ba" inji shi.
Abubakar Usman Dutsi shima daya ne daga cikin masu neman takarar ta Ciyaman na Dutsi, ya bayyana cewa, "Duk wani Dan jam'iyyar APC bayan su yake, saboda tun a lokacin APP suke cikin jam'iyyar tazo ANPP ta koma CPC yanzu kuma tana APC amma basu barta ba, sana aka saka masu da wannan rashin adalcin."
"Muna mika koken mu ga mai girma Gwamnan jihar Katsina da shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina da masu ruwa da tsaki a matakin jiha, da su san halin da ake ciki a karamar hukumar Dutsi, su san cewa ba sasanci akai a karamar hukumar Dutsi ba, Murdiya da Zalunci aka yi, kuma muna kira ga resu da su shiga tsakani kafin wuri ya kure. Inji Sanusi Haruna Aliyu.
A ranar Asabar 4 ga watan Mayu ne gwamnan jihar Katsina malam Dikko Umar Radda ya jagoranci wani zama na musamman da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a fadin jihar Katsina akan zaben kananan hukumomi inda aka tattauna al'amura da dama gami da bada shawara daga gwamna radda cewa akwai hanyoyin uku da dokar jam'iyyar APC ta yadda ayi aiki dasu a yayin fidda dan takara, sasanci, 'Yar Tinƙe (Kato bayan Kato) gwamnan yace yafi karfafa cewa aje ayi sasanci don fito da yan takarar ko wace karamar hukuma a jihar.
Ibrahim Sirika Abubakar, Bashir Usman Dutsi, Sanusi Haruna Aliyu, Dukkanin su 'yan takarar Ciyaman ne na ƙaramar hukumar Dutsi da tawagar su, suka ziyarci Ofishin Katsina Times don gabatar da korafe-korafen su.
Muna da cikakken Rahoton na bidiyo da zamu kawo maku.