SANARWA SAUKAR RUWAN SAMA DAGA KUNGIYAR MANOMA
- Katsina City News
- 05 May, 2024
- 641
May 5, 2024
Kungiyar Manoman gaskiya ta jihar katsina wato AFAN na kira ga manoma jihar da suyi amfani da irin shuka me kyau Wanda ke jure yanayi a wannan damuna dake gab da kamawa
Shugaban kungiyar Rt. Hon. Ya'u Umar Gwajo-Gwajo ne ya bayyana haka a wata sanarwar da aka rabawa manema labaru Inda yace kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta Sanar da jadawalin yadda damina zata fara sauka da Kuma daukawar ta a duk jahohin Nigeria a wannan shekara, hakanne yasa ya yi kira ga manoman jihar katsina da suyi amfani da irin shuka Mai inganci Wanda ya yi dai dai da yanayin da akai hasashen saukar daminar da Kuma yin shuka da wuri dan kaucewa yin asara.
Shugaban kungiyar yace hasashen hukumar ya nuna cewa a jihar katsina za'a fara ruwan shuka a yankin Funtua daga ranar biyar ga watan Yuni ya kare ranar ashirin da bagwai ga watan October.
Gwajo-Gwajo ya Kuma ce a Shiyyar Daura hasashen ya nuna za'a fara ruwan shukar daga ranar ashirin da biyar ga watan Yuni ya kare sha biyar ga watan October
Shugaban kungiyar munoman ya Kara da cewa hasashen ya nuna a shiyyar Katsina in nan za'a fara ruwan shukar daga ranar sha bagwai ga watan Yuni zuwa sha tara ga watan October na wannan shekara.
Dan haka ya bukaci manoma da su kiyaye Kuma subi dokokin da hukumar da kindaya dan samun ingantattar damina.
Gwajo-Gwajo ya Kuma ja hankalin manoman jihar dasu rika tintibar masana harkokin noma kan duk Wani abu da basu gane ba inda daga karshe ya yi Addu'ar Allah ya bamu damina Mai albarka ya kaudar da duk wata matsala a wannan damina dake tafe
Daga nan ya jinjinawa Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda kan daukar Malaman gona 722 gami da basu babura dan su zagaya su fadakar da manoman jihar dabarun noman zamani.
Ya Kuma Yabawa Gwamnan kan aniyar Gwamnatin sa na sawo takin zamani na naira milliyan dubu goma dan rabawa ga manoman jihar Wanda aka dade ba'ayi ba
Shugaban kungiyar ya Kuma yi kira ga Gwamnan jihar da ya cigaba da talkafama Manoman jihar da kayayyakin noma dan bunkasa harkokin noma a jihar.
Daga karshe ya bukaci Al'ummar jihar dasu cigaba da yin addu'o'i dan Kara samun zaman lafiya a jihar dama kasa baki daya.