JAHAR ZATA KAFA HUKUMAR TSARA TATTALIN ARZIKI
- Katsina City News
- 03 May, 2024
- 513
@ Katsina Times
A ƙoƙarin sa na inganta rayuwar al'umma, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da kafa Hukumar Tsara Tattalin Arziki a jihar.
Gwamnan ya jagoranci wani zama na musamman na Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara a ranar Alhamis a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa majalisar ta amince da wasu muhimman ayyuka da za su amfani al'ummar Jihar Zamfara.
“A wani zama na musamman da Majalisar Zartarwa ta yi, Gwamna Dauda Lawal ya amince da kafa Hukumar Tsara Tattalin Arziki ta Zamfara. Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare Hon. Abdulmalik Abubakar Gajam ne zai jagoranci hukumar.
“Hukumar Tsara Tattalin Arzikin Jihar Zamfara za ta ɓullo tare da aiwatar da tsare-tsare na tattalin arziki domin bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a jihar, kuma ana sa ran za ta taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da tattalin arzikin yankin gaba da bunƙasa rayuwar al'umma.
Sanarwar ta ce, “Haka zalika, hukumar za ta taimaka matuƙa wajen ganin jihar ta cimma dukkan manufofinta na tattalin arziki domin ci gaban al’ummar Zamfara.
"Hukumar za ta kasance ƙashin baya na haɗin gwiwa, wanda za ta ƙunshi dukkan 'yan majalisar zartarwa na Jiha, shugabannin ƙananan hukumomi, da manyan masu tafiyar da tattalin arzikin jihar tare da ma'aikatan gwamnati. Hukumar tana kamanceceniya da Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa."