Tatsuniya (16) Labarin Kawancen Kyanwa Da Bera
- Katsina City News
- 01 May, 2024
- 659
Ga ta nan, ga ta nanku.
Kyanwa da Bera dai ne suka yi kawance, suka kuma yi shawarar cewa Ya kamata su tara kayan abinci da za su rinka ci idan lokacin hunturu ya zo.
Suka kuwa zartar da wannan shawarar.
Suna nan, sai rannan Bera ya ce da Kyanwa zai je bikin Kanwarsa. Da ya fita sai ya nufi rumbun abincin da suka tara, ya ci har sai da ya koshi.
Da ya dawo gida sai Kyanwa ta yi masa maraba, ta tambaye shi, “Me aka
samu ne?"
Bera ya dubi Kyanwa ya ce: “Abin da aka samu shi ne, wuyar aiki ba a fara ba!"
Aka yi murna aka watse.
Bayan 'yan makwanni kuma Bera ya je wani sunan, ya bi ta Rumbu ya ci har ya koshi.
Da dawowa gida sai Kyanwa ta tambaye shi: "Yau kuma wa aka Samu? Sai Bera ya dubi Kyanwa yana murmushi ya ce: "Yau kuma an
sami kwanci-tashi ba ta bar komai ba."
Duk abin da Bera ke yi dai Kyanwa ba ta san komai ba. Da Bera ya je gidan suna na uku ya dawo, sai Kyanwa ta nemi sanin abin da aka samu, sai Bera ya ce: an sami ta faru ta kare.
A tafiyar suna na hudu Bera ya dawo da fuska a murtuke. Ita ko kyanwa ta tambayi sunan jariri da goron suna.
Maimakon Bera ya ba ta jawabi kamar yadda ya saba, sai ya fara yi mata wani kallon raini, kuma ga shi tana jin yunwa, tana jiran ya kawo mata abincin suna.
Da ta ga alamun babu abincin nan, kuma Bera yana yi mata kallon raini, sai haushi ya kama ta ta fusata ta ce: "Kai ka cika surutu da fitina."
Kafin a ce haka, ta yi carab ta far masa, ta kama shi ta cinye.
Karya da dadin ji, amma ba na yi tun da Gizo yana nan.
Kurunkus.
Mun dauko wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman