MATA AKWAI HALASCI! Labari Mai Taba Zuciya

top-news

#Darasin Rayuwa @Katsina Times

Bayan kammala makarantar Sakandare, na yi aiki da wani gidan abinci, wata rana da safe sai ga wani wanda ya saba zuwa gidan abincin yana sayen kalacin safe ya zo da wata yarinya,  suka ci kalaci tare sai ya ce min don Allah za ta jira shi har a taso aiki. Ya ce ya ba ni amanarta, kar in bari kowa ya yi mata magana.

Mutumin nan ya zo da yarinyar nan sau uku, tsawon kwanaki uku. Kullum za ta jira sai wajen karfe 2:00 zai dawo su ci abincin rana sai ya tafi da ita.

A rana ta uku na kalli yarinyar nan tsaf na ga karama ce sosai. Ni a lokacin ina tsammanin ba ni wuce shekaru 16-17 ba, amma wannan yarinya daga ganin ta ba ta wuce 12-13 ba, in ta yi gudu 14.

Sai na tambaye ta me ya hada ta da wannan mutumin? Sai ta ce guduwa ta yi daga garinsu za a yi mata  auren dole, sai aka kai masa ita da niyyar ta dan zauna a wajensa. 

Wa ya kai masa ke? Na tambayae ta. Ta ce wani dan kamasho ne a tasha. Ina ya ajiye ki? Sai ta yi shiru.

A nan na fara yi mata wa'azi, na jawo hankalinta cewa sai ta ba ta wa iyayenta rai ta zo tana kyautata wa wani kato?

Sai ta ce ita ba ta son wanda ake son a hada su, amma in ni na amince zan zo gidansu a yi mana aure za ta koma gida. 

Na amince mata da hakan (amma a zuciya ta ba da gaske nake ba. Ina so ne kawai ta koma gida).

Na tsara mata yadda za ta fito da shirin komawa ba tare da ta fada wa wanda ya ba ta masauki ba.

Na kwana da tunanin Allah ya sa mu yi nasara kar wannan mutumin ya gane ko kuma ya ki fitowa da ita.

A rana ta hudu, kawai sai ga shi sun zo tare. Muna hada ido ta kyafta mani ido, na san ta fito da niyyar komawa gidansu.

Bayan sun gama kalaci kamar kullum ya ce ta jira shi. Ya hau babur dinsa ya tafi wajen aiki.

Ina ganin ya tafi na ce kin shirya? Ta ce tsaf! 

Sai na nuna mata hanyar da za ta bi har zuwa tasha. Zan ba ta kudi ta ce a'a tana da kudin da yake ba ta kullum, wai ko da tana bukatar wani abu.

Na ce kar ta hau komai ta taka kasa har tasha babu nisa daga inda muke.

Na fito wajen ina kallon ta tana tafiya, tana waiwaye na ina kallon ta har ta bace.

Na dawo wajen aiki na na yi zamana. 

Karfe 2 sai ga mutumin ya dawo kamar yadda ya saba. Ya ce ina bakuwarsa? Na ce ta ce min za ta mike kafafu, amma ban san inda ta nufa ba.

Nan ya yi ta jira har 4 ba ta dawo ba. Ya yi ta surutai, har da yi min barazana, amma na yi banza da shi.

Sai da ya yi kwanaki kullum ya zo sai ya yi maganar YARINYAR.

Wani lokacin ya shafa mani zuma a baki in har na fada masa inda take. Wani lokaci kuma ya yi min barazana.

Sai bayan da ta tafi da kwana daya na fahimci cewa ashe sam ban ma tamnbayi sunanta ba. Ban kuma tambayi garinsu ba. Wa wani bayani nake da shi a kanta. A lokacin na fahimci ni da ita har abada.

Tun ina tuna ta akai-akai har na manta da ita.

Na sha mafarkin ko ina zan gan ta? Na dan yi labarin da abokaina a lokacin. 

Bayan wata daya da faruwar lamarin na samu gurbin karatu a gaba da Sakandare na bar aikin na tafi. Na ma bar garin namu na koma makarantar. 

Wani lokacin in na tuna ta, sai in ce ko ta dawo ba ta iske ni.

BAYAN KUSAN SHEKARU 30

Wata rana ina zaune a ofis dina sai na ji an ce wane muke son gani. Sai aka ce yana ciki. Sai ga wata mata ta shigo da wasu 'yan mata guda biyu da karamar yarinya da samari majiya karfi biyu ga wani kato ya tare bakin kofar yana zare idanu. 

Sai matar nan ta ce ka san ni? Cikin tsoro, saboda ban san da wacce ta zo ba na ce, Wallahi ban san ku ba, ban kuma taba ganin ku ba.

Matar ta lura akwai tsoro a fuskata. Sai ta ce 'calm down!' Wadannan 'ya'yana ne. Wancan na bakin kofar direbanmu ne, ya tsaya ne don ya tabbatar da inda muke nema nan ne?

Da ta lura bayanan ta ba su cire tsoron da ke fuskata ba. Sai ta ce ka tuno wata yarinya da ka taba taimako ta koma gidan su lokacin kana aiki a wani gidan abinci? 

Nan take na tuna, na ce kwarai kuwa na tuna.

Ta ce; "To ni ce! Wadannan kuma 'ya'yana ne. Na kawo su ne su gode maka."

Na kalle ta na ga lallai ita ce. Sai dai girma ya fara kama ta.

Ta zauna yaran nata ma suka zauna. Na kasa magana. 

Na ce a sawo masu ruwa. Ta ce a'a ruwa leda da ke wani mazubi na ofis dina duk za su sha.

Can cikin raha da barkwanci sai ta ce; "Ba ka cika alkawali ba." 

'Ya'yanta suka fashe da dariya. Suka ce oh...Mama!

Cikin tsoro da mamaki sai na ce mata ai bayan tafiyarki na gano cewa ban tambayi sunanki ba. Ban tambayi garinku ba. Ban kuma tambayi sunan iyayenki ba. 

Ta ja numfashi ta ce ni ma na gano hakan. Tana dariya tana shafa kafar ta.

Sai na yi na ta maza na ce me ya faru bayan rabuwarmu? 

Ta ce; "Na je tasha na hau mota har zuwa gidanmu. A gida na iske an tara malamai suna ta addu'ar Allah ya dawo da ni. Na ga yadda hankalin iyaye da 'yan'uwa da ma mutanen garinmu ya tashi, sai na ce na amince a daura mana auren da wanda na gudu saboda shi. In dai hakan ne zai faranta maku rai, ya kwantar maku da hankali, to na yarda a yi auren. 

"Shi ne uban wadannan yaran, kuma a tare muke da shi yana wani masaukin baki da muka sauka."

Ta ce; "Kwata-kwata mantawa na yi da kai, sai lokacin da na haihu yarinyata ta biyu na fara tunawa da kai da irin taimakon da kai min. Daga nan ne na fara yi maka addu'a da fatan Allah ya sanya in kara ganin ka kafin mu bar duniya."

Ta ci gaba da cewa: "Yadda na gano inda kake shi ne hotonka da ya rika yawo ka rataya maciji, sai  'ya ta ta ce 'Hajiya kalli wani mutum rataye da maciji!' Ina kallon hoton na gane ka.

"Nan da nan na ce ta gano min wanene shi? Kuma a ina yake? Ita da 'yan'uwanta sukayi ta latse-latsen wayarsu, har da buga wa ga wasu abokan karatunsu waya. Cikin mintuna sai ga bayanin har da wannan ofis din naka."

Muna zaune sai mai gidanta ya zo. Babban mutum ya girme ni sosai. Muka gaisa. Ya ce: "Kai ne ka ceci Maman su Hannan?" 

Na ce, a'a. Allah ne ya cece ta. Ya yi amfani da ni ne kawai. Muka fashe da dariya. Shi ma ya zauna.

SAURA KIRIS DA SUN RABU SABODA NI
Ta fada min cewa, ba ta san ya aka yi ba, amma sai da ta shekaru sama da 10 ta manta da ni da kuma gudun da ta taba yi saboda kar ta auri uban ya yanta.

"Wani lokaci sai in ji akwai abin da nake son in tuna, amma na manta. Wata asuba na gama Sallah ina kallon yara na ina jin dadi ina ganin yadda maigidana ke kula da ni ina masu addu'a, kwatsam sai ka fado min a rai. Ban san lokacin da na daga hannu na ce, ya Allah! Kai ne ka san inda yake, ko yana da rai ko ya mutu. Kai ka san halin da yake ciki. Allah ka kasance tare da shi. Cikin rashin sani ina kuka ina addu'a, ashe mijina ya dawo daga masallaci ya shigo har ya zauna kusa da ni ban sani ba. 

"Bayan na gama. Sai kawai ya rikice. Sai na fada masa waye wannan? Kuma a ina yake? 

"Tsoron me zai biyo baya, don na san halin mijina, sai na ki fada masa. Wasa-wasa ya ce a kai ni gida sai ya zo.

"A gida, naki fada masu sai bayan da ya zo ga ni ga iyaye na ga nasa, kuma ga shi.

Na ce masu don Allah kun tambaye ni ina na je bayan na gudu? Kun tambaye ni ya aka yi na dawo?" 

Suka ce a'a. Shawara aka yi aka ce wannan magana kar ma a tada maki ita.

Ta ce: "Da na gudu, na fara fadawa wani mugun hannu wanda da a ce na dade wajensa ku da gani na har abada."

Ta ce daga hannun mugun hannun na hadu da wani bawan Allah shi ne ya karfafa mani gwiwar in dawo gida. ta bayyana masu komai da yadda a kai."

Ta ce: "Tun da na tako gidan nan na manta da bawan Allah nan. Sai ranar da ka ji ni ina addu'a gare shi. Ina yi ma 'ya'ya na da kai mijina addu'a kawai ya fado min a rai. Yau shekaru 10 ke nan.

"Ban san inda yake ban ma tuna shi ba, ban kuma san me ya sa ba, amma tun da yanzu na tuna shi tabbas zan rika yi masa addu'a.

"A zaman duk aka fahimce ni, har mijina ya ba ni hakuri. Kuma daga nan muka koma gida tare."

Ta fada mani cewa ta haihu da yawa, amma Allah ya dauki ransu biyar kawai suka rage.

Bayan sun huta na raka su har motocin su biyu daya na dauke da yaran daya, kuma matar da mijinta da karamar 'yarsu. Suna shan wata kwana suka dago min hannu baki daya. Ban san lokacin da kwalla ya cika man idanu ba. 

Allah ya ba su zaman lafiya, ya dayyaba zuriyarsu.

A lura: Wannan labarin ba kirkirarre ba ne, kuma da yardar matar da mijinta aka rubuta shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *