BANBANCHI TSAKANIN MAGUZAWA, HABE, FULANI DA JIHADIN MUSULUNCHI.
- Katsina City News
- 25 Apr, 2024
- 370
Mulki ko shugabanchi a Kassr Katsina ya faro ne daga Sarakunan Durbi Takusheyi, wadanda yawancin marubita Tarihi sun nuna MAGUZAWA su, an dauke a matsayin MAGUZAWA ko Arna, saboda suna da addinin su Gargajiya, Wanda bana MUSULUNCHI. Suna bauta iskoki da Tsahehe, a wancan lokacin. Haka akai ta tafiya har zuwa tsawon lokaci, kamin bayyanar MUSULUNCHI a Katsina. A lokacin suna da al'adar fitar da shugaba, musamman ta hanyar Kokowa, Wanda duk bayan shekara anayin Kokowar Tsakanin Sarki da Wanda ya fito takara. Idan Sarki ya kada ka zai ci gaba da Sarautar shi, idan Kuma kai ka kada sarki to zaka yanka Sarki ka zama Sabon Sarki. Ana cikin wannan halin ne Sai aka samu bakunchin Muhammadu Korau, Wanda asalin su, Wangarawa daga Kasar Mali, suka fara zama Yandoto, daga Yandoton ne, yazo Katsina acikin shekarar 1348, yayi Kokowa da Sanau ya kada shi ya zama Sarkin Katsina Musulmi na farko daga Zuruar Wangawa. Wannan shine farkon mulkin Habe a Katsina.
2. Minene Habe? Habe kalma ce ta Fulanchi da take nufin Wanda ba bafullatani ba, wannan shine Maaanar Habe. Sarakunan Habe sun mulki Katsina tun daga shekarar 1348 har zuwa 1806, lokacin da Masu Jihadi suka Kore su daga Katsina. Wane ci gaba Katsina ta samu a lokacin mulkin Habe? An samu ci gaba a lokacin mulkin Sarakunan Habe, musamman ta bangaren addini da Kuma Kasuwanchi. Misali da farko an Gina Masallacin Gobarau,Wanda ya zama babbar centre ta addinin MUSULUNCHI a Kassr Hausa, hakanan Kuma an fadada Kasuwanchi Sahara tsakanin Kasar Katsina da sauran Kasashe, ta fannin mulki an Gina Gidan Sarautar Katsina Mai suna Gidan Korau Wanda har yanzu, Sarakunan Katsina suna amfani dashi. Kadan kenan daga cikin ci gaban da Katsina ta samu a lokacin Habe.
Abin tambaya anan shine, Mi ya faru an karshen mulkin Habe, har ya jawo Jihadin musulunchi? Acikin Karna 19 ne (19th Century) Shehu Usman Danfodio yayi Kira da a kaddamar da Jihadi sannan a Jaddada addinin MUSULUNCHI a Kassr Hausa da wasu kasashen kamar Nufe, da Yoruba da sauran su. A karshen mulkin Habe an samu matsalolin musamman hada addinin musulunchi da addinin Gargajiya( Mixing Islam with traditional religion) wannan ya faru a mafi yawan Kasashen Hausa, Wanda Marubuta Tarihi irinsu, Dr. Yusuf Bala Usman sun rubuta, Professor Murry Last ya rubuta haka, Professor Dahiru Yahaya ya rubuta haka da sauransu. A kan wannan dalilinne a Katsina Mujahidai ukku da mabiyansu sukayi takakkiya har Sokoto wajen Mujaddadi Shehu Usman Danfodio domin anso tutar umarnin kaddamar da Jihadi da Kuma Jaddada addinin Musulunchi. Bayan sun dawo Katsina an gwabza Yaki inda akayi nasara akan Sarakunan Habe, suka gudu suka koma Dankama daga nan Sai Damagaram, Sai Maradi inda suka sabuwar Masarautar su Mai suna Sarkin Katsina Maradi.
Wannan yunkurin ne yayi sanadiyyar karshen mulkin Habe a Katsina. Aka kafa Daular musulunchi a Katsina a karkashin Jagorancin Malam Ummarun Dallaje. Wane irin ci gaba Jihadi ya kawo a Katsina? Da farko an jaddada addinin musulunchi, 2. An kafa Shariar Musulunchi wadda ta rayu tsawon shekara dari, 3. An kafa mulki irin na Tarayya, 4. An Kara fadada harkar Kasuwanchi tsakanin Katsina da sauran Kasashe, musamman larabawan North Africa, Professor Babajo ya bayyana haka acikin littafin shi Mai suna Trade Diplomacy Bankin and Finance, inda ya nuna cewa Ahmad Abul Gaisu shine babbban Wakilin Kasuwanchi tsakanin Katsina da Algeria a lokacin mulkin Ummarin Dallaje. An samu ci gaba da dama a lokacin, Wanda suka rayu har tsawon shekara dari 1806 zuwa 1906.
Daga karshe ina so mu gane cewa, idan akace Habe ba ana nufin Arna ko MAGUZAWA ba. Sarakunan Durbi Takusheyi sunyi mulki a Katsina kamin zuwan musulunchi, saboda haka an daukesu a matsayin Arna ko MAGUZAWA, Sarakunan Habe da suka biyo bayansu, Musulmi Amma a karshen mulkinsu, an samu matsalolin musamman hada addinin musulunchi da addinin Gargajiya Wanda Akan shine Shehu Usman Danfodio ya kafa hujjar shi ta yakar su. Kuma ya samu nasara akan su. Ya kafa centralize government Wanda ya hade gaba dayan Kasashen Hausa da wasu makwabtanra a wuri guda Kuma suna ansar umurnin su daga Sokoto wadda ta zama Hedikwata a wancan lokacin.
Musa Gambo Kofar soro